Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fada ajiya Asabar cewa Amurka zata bada taimako a duk inda zata iya, yayin da yake ganawa da masu tattuanawa na bangaren gwamnatin Afghanistan a Qatar, a daidai lokacin ake ganin alamun samun nasarar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban.
Zababben shugaban Amurka Joe Biden, ya yi kira ga majalisar dokokin Amurka da ta yi dokar agajin gaggawa ta biliyoyin dala a kan taimakon COVID-19 kafin karshen shekara, a cewar babban mai bashi shawara, wanda ya yi kashedi jiya Juma’a cewa yanzu ba batun bata lokaci.
Ga dukkan alamu, gwamnatin Najeriya da kafar labarai ta CNN za su sa kafar wando guda, biyo bayan irin labaran da kafar ta CNN ta yada game da zanga zangar EndSARS, da gwamnatin Najeriya ke ikirarin cewa akwai na karya ciki, tare da shan alwashin daukar mataki.
Birnin New York ya umarci makarantu su rufe ranar Laraba, yayin da garin ya sami karin yawan masu kamuwa da coronavirus kwanaki bakwai a jere sama da kashi uku cikin 100.
Shugaban ya yi ikirarin cewa kalaman Chris Krebs kan gamsuwa da sakamakon zaben 2020 ba daidai ba ne.
Masu zanga zanga sun yi taro a Washington a jiya Asabar domin nuna goyon baya ga shugaba Donald Trump da zargin da ya yake yi na tabka magudi a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba da babu hujja.
Jiya Lahadi, a karon farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna ya amince da cewa dan takarar Demokrat Joe Biden "ya lashe" zaben shugaban kasa kusan makonni biyu da suka gabata, amma sanadiyyar magudi.
Yankin Navajo a Amurka ya sanya matakan kulle tsawon makonni 3 saboda karuwar yaduwar cutar COVID-19.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yabawa ci gaban da ake samu wurin samar da maganin rigakafin coronavirus a jiya Juma’a, a jawabinsa na farko a bainin jama’a tun bayan lokacin da kafafen yada labarai suka ce tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya lashe zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.
Akwai muhimman dalilan da yasa ya kamata a saka kyallen rufe huska a wannan lokaci fiye da kowane lokaci, a cewar cibiyar yaki da cuta mai yado a Amurka ta CDC.
Babban jami’in zabe a jihar Georgia da ke kudancin Amurka ya ba da umarnin a sake kidayar kuri’un zabe da hannu wanda aka yi tsakanin Shugaba Donald Trump da zababben Shugaban Joe Biden.
Amurka ta kara sumun adadin tarihi na masu kamuwa da coronavirus a rana guda.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.