Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Kori Krebs Daraktan Cibiyar Tsaron Yanar Gizo Ta Amurka


Shugaban ya yi ikirarin cewa kalaman Chris Krebs kan gamsuwa da sakamakon zaben 2020 ba daidai ba ne.

Ta shafinsa na twitter Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da korar Krebs, daraktan cibiyar tsaron yanar gizo ta Amurka, saboda bayanan da Krebs din ya yi a kwanan nan game da zaben kasar.

Krebs ya sha karyata zarge-zargen magudin kuri’u a ‘yan makonnin da suka gabata, ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, “game da zarge-zargen an yi ba daidai ba a tsarin zaben, kwararru masu kula da tsaron kuri’u 59 dukkansu sun yarda cewa, a kowanne zargi da muke da masaniya akai, ko dai babu wata kwakkwarar hujja da aka gabatar ko kuma dai babu makama a zargi-zargen.

A jiya Talata ne Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa bayanan Krebs “ko kadan ba daidai ba ne” ya na mai zargin an tafka magudi sosai a zaben.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

"A saboda haka, ba tare da bata lokaci ba, an sauke Chris Krebs daga mukamin daraktan cibiyar tsaron yanar gizo ta Amurka, a cewar sakon shugaban."

XS
SM
MD
LG