Kusan mutane miliyan 54 ne suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya, a cewar rahoton cibiyar samar da bayanan coronavirus ta Johns Hopkins a yau Lahadi.
Amurka, India, da Brazil ne ke ci gaba da kasancewa kan gaba a matsayin wuraren da cutar ta fi kamari. Amurka na da kusan adadin mutun miliyan 11 da suka kamu da cutar, yayin da India ke da miliyan 8.8, Brazil kuma miliyan 5.8.
Ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamba India ta sanar da samun mutun 41,100 da suka kamu da cutar cikin sa’o’I 24 da suka gabata.
Karuwar yaduwar cutar a Amurka ya sa yankin Navajo daukar matakan kulle tsawon makonni 3 daga ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba.
Facebook Forum