Kungiyoyi da daidaikun jama'a na cigaba da gudanar da zanga-zanga a ciki da wajen Nijeriya na neman a sako 'yan matan da aka sace a makarantar Chibo da ke jihar Borno.
Hukumomin arewacin Najeriya sun ce har yanzu babu labarin 'yan mata 'yan makaranta dari biyu da saba'in da shida daga cikin wadanda aka sace a wata makaranta a watan jiya.
Mrs. Kema Chikwe wadda itace shugaban matan PDP ta kasa, ta bayanna shakkar sace daliban Cibok.
Gwamnan Jihar Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi bakoncin maza da mata masu neman Shugaban Kasa ya dauki matakin nemo dalibai mata da aka sace su sama da 200 a makarantar Sakarandaren Cibok dake Jihar Borno.
Daruruwan mata ne sukayi zanga-zangar lumana da maracen jiya a Kano dangane da abin da suka kira halin ko in kula da gwamnatin Tarayyar Najeriya ke yiwa batun ‘yan mata 234 da ‘yan bindiga suka sace a kwalejin ‘yan mata ta garin Chibok na jihar Borno fiye da makonni biyu da suka gabata.
Dubban mata daga kowane bangare na Najeriya sun hallara a Abuja, babban birnin tarayya, domin nuna bakin ciki da fusatarsu game.
Shuwagaban majalisar dattawan Najeriya David Mark, da kakakin majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal sun gana da gungun mata masu zanga-zangar lumana na neman hukumomi su dauki mataki domin ceto mata dalibai wadanda ‘yan bindiga suka sace a makarantar Sakandare dake Cibok sama da makonni biyu kennan.
Mata ‘yan asalin Cibok mazauna birnin Tarayya sunyi tururuwa zuwa Majalisar Kasa sanye da bakaken riguna, inda suka kai kukansu game ‘ya’yansu mata sama da 200 da aka sace a makarantar Sakandare dake Cibok.
Majalisar kasa ta ce Gwamnatin Tarraiyya ta samo yan matan nan da yan ta'adda suka sace ko suna da rai ko babu.
Kowace ranar Allah takaicin iyayen dalibai matan da aka sace a Chibok sai karuwa ya ke yi saboda rashin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki da kuma jita-jita daban-daban da su ke ta ji.
Domin Kari