A lokacin da yake tarbar gungun masu gangamin neman gwamnati ta dauki kwararan matakai domin ceto dalibai mata sama da 200 da aka sace a makarantarsu ta Sakandare dake Cibok, gwamnan Jihar Lagos Babatunde Fashola ya bayyana matsayinsa.
#BringBackOurGirls
Jami’an tsaron Najeriya sunce suna da isassun kayan aiki na amfani da su wajen neman daruruwan dalibai mata wadanda aka sace daga makarantarsu ta Sakandare a Cibok.
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International tace shaidu da ta tattara sun bayyana cewa dakarun tsaron Najeriya sun san cewa ‘yan bindiga sun doshi garin Cibok a daren 14 ga watan Afrilu, amma suka kasa daukar matakin yin rigakafi, duk da gargadin da suka samu.
Alhamis dinnan, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya dauki alwashin fito da dalibai sama da 200 da ‘yan bindiga suka sace, yayin da lamarin sace daliban ya mamaye jawabin bude taron da ya kamata ace ya mayar da hankali ne akan nuna albarkar nahiyar Afirka, dangane da zuba jari a kasar da tafi kowace kasa karfin tattalin arziki a nahiyar.
Wani dattijo a Najeriya yace a shirye yake ya sadaukar da kanshi da ‘yan uwanshi dattawa wadanda zasu yarda, domin musayar daliban Cibok da aka sace, a wajen ‘yan bindigan da suka sace su. Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta tattauna da wannan dattijo.
‘Yan majalisar Amurka na ci gaba da nuna hasalansu kan fiye da ‘yan makaranta, mata dari biyu da ‘yan tsattsauran ra’ayin addini suka sace.Sanata Susan Collins, ‘yar kungiyar Republican wace ta mika kudirin kare mata a duniya tana cikin bidiyo.
A dai-dai wannan lokaci da shuwagabannin duniya suke kawowa Najeriya dauki, wajen gani an nemo daliban Cibok mata wadanda aka sace su kusan 300 a makarantarsu ta Sakandare, dan siyasa, tsohon shugaban kasa kuma daya daga cikin shuwagabannin jam'iyyar APC Janar Muhammadu Buhari mai ritaya ya fitar da sanarwa.
Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, ta soki gwamnatin Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan musamman ma akan arewacin Najeriya, tana cewa gwamnatinshi tayi facaka da arzikin man fetur dinta, kuma haka ya saka cin-hanci da rashawa yayi karfi sosai a kasar mai fama da rigingimu.
Manyan malaman Musulunci kuma jami’an kungiyoyin ‘yancin bil adama na duniya sunyi Allah wadai da sace dalibai mata, suna kira haka a matsayin “sabanin addinin Musulunci”, kuma suna kira a sako daliban na Cibok.
Domin Kari