Ana zargi cewa masu goyon bayan Jonathan sun rabawa wasu mata Naira 1.000 daya-daya domin kawo cikas ga zanga-zanga akan ‘yan matan da aka sace, a Abuja. Daya daga cikin irin wadannan matan ta kowa da abin da ya samu amma ita kudin mota ne kawai.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, tace idan har Amurka ta san inda ake garkuwa dasu ba zata fada ba.
Maimakon yin bikin ranar yara ta duniya kamar yadda aka saba kowace shekara gwamnatin jihar Neja ta mayarda ranar ranar addu'o'i sabili da yaran da kungiyar Boko Haram ta rutsa da su da kuma 'yan mata fiye da dari biyu da take garkuwa da su.
Daya daga cikin shuwagabannin Kungiyar Dattawan Chibok a Jihar Borno dake Najeriya, yace kwamitin da shugaban kasa ya kafa saboda daliban da aka sace ya gaza haduwa da kungiyar, da kuma kai ziyara Chibok duk da cewa kwamitin yayi alkawarin yin haka.
Wani babban jami'in sojin Nijeriya ya ce yanzu hukumar sojin kasar ta san inda masu kaifin kishin Islama su ke tsare da dalibai 'yan mata sama da 200 dinnan, to amma ya ce zai yi wuya a yi amfani da karfi wajen bukutar da su.
Yayin da yake karbar malaman da suka yi zanga-zangar lumana domin nuna takaicinsu akan sace daliban Chibok gwamnan Sokoto Aliyu Magatakardan Wamako yace yanzu ba lokaci ba ne na dorawa kowa laifi.
Wasu iyayen daliban da aka sace sun bi sawun 'ya'yansu har sun hangosu a karkashin bishiya amma sojoji sun kasa su rufa masu baya domin su kwato daliban kafin su yi nisa.
Tosffin jami'an siyasa mata da wadanda suke kan gado sun yi taron karfafawa mata gwiwa su cigaba da karatunsu domin kada su bari abun da kungiyar Boko Haram tayi a Chibok ya karya masu gwiwa.
Kwana bayan girke jami’an sojin Amurka a Chadi, tuni sun fara aika jirage marasa matuka a ciki domin neman daliban nan mata sama da 250 da ‘yan Boko Haram suka sace.
Domin Kari