A wani sabon bidiyo da mutumin da yace shine shugaban kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, ya fitar a baya-bayannan, Abubakar Shekau yace ya musuluntar da wadannan mata, wadanda yace ya sato su, sannan yana bukatar ayi musaya dasu.
Yayin da 'yan jam'iyyar APC suka kaiwa gwamnan jihar Borno gaisuwar jajantawa sabili da daliban Chibok da aka sace gwamna Shettima yace idan sadakar da ransa zai kawo wa al'ummarsa da kasar zaman lafiya to ashirye yake yayi hakan.
Masu zanga-zanga a cikinsu harda tsohuwar Ministan Ilimi, sun jaddada ‘yancinsu na gudanar da taron lumana, yayin da suke kira a dawo da dalibai su sama da 200 da ‘yan bindiga suka sace.
Wasu daga cikin gungun ‘yan mata daliban makarantar sakandaren da ‘yan ta’adda suka kaiwa hari a jihar Bornon Nigeria, sun yi bayanin yadda suka yi sa’ar kubuta daga kangin daga ‘yan Boko haram suka yi wajen shirya kamesu a gidajen kwanansu na makaranta.
Yayin da jami’an kasa da kasa suka riga suka fara isa Najeriya domin taimakawa wajen gani an ceto daliban Cibok, mafi yawancin gwamnoni da shuwagabanni basu ce komai ba game da lamarin, musamman ma ta bangaren nuna alhini da jajantawa mutanen Najeriya.
Daga cikin matakan da shuwagabanni suke dauka a lokutan tashin hankali da rigingimu, akwai ziyarar gani da ido, domin jajantawa da nuna alhini. Tambayar anan itace yaushe Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya zai je Cibok?
A wani matakin ba-sabam ba, Mes. Obama ta gabatar da jawabin mako-mako na shugaban inda ta maida hankali kan sace dalibai mata na Chibok su fiye da 300.
A lokacin da yake tarbar gungun masu gangamin neman gwamnati ta dauki kwararan matakai domin ceto dalibai mata sama da 200 da aka sace a makarantarsu ta Sakandare dake Cibok, gwamnan Jihar Lagos Babatunde Fashola ya bayyana matsayinsa.
#BringBackOurGirls
Jami’an tsaron Najeriya sunce suna da isassun kayan aiki na amfani da su wajen neman daruruwan dalibai mata wadanda aka sace daga makarantarsu ta Sakandare a Cibok.
Domin Kari