WASHINGTON, DC —
Matan da adadinsu ya kai dubu uku wadanda tsohuwar ministan Ilimi Oby Ezekwesili ta jagoranta, sun fara zanga-zangar ne daga dandalin “Unity Fountain” a nan birnin Abuja zuwa Majalisar Kasa, wanda tazararsu ya kai kilomita hudu da rabi.
Shuwagabannin majalisar sun nuna alhininsu game da sace daliban mata, kuma sun bayanna wa matan cewa suna tare dasu. Sun bayanna cewa sun kira shuwagabannin hukumomin tsaro domin amsa tambayoyi a gabansu.
Kakaki Tambuwa da Mr. David Mark sun tabbatar cewa zasu gabatar da kukan wadannan mata cikin gaggawa ga shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Matan dake sanye yawancinsu da jajayen kaya sun rike alluna dake dauke da alamu kamar “Gwamnati ta Gaza” , da kuma kira akan gwamnati tayi yunkurin ceto daliban mata.
A cikin wadanda suka hallarci taron, akwai uwar gidan dan siyasa Atiku Abubakar, wanda ya taba yin mataimakin shugaban kasa. An samu hallarcin maza kusa dubu biyu suma wadanda suka taka tare da matan domin kira ga shuwagabanni a nemo wadannan yara.
Zanga-zangar da aka shafe sama da sa’o’i uku ana yi, an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da lumana, duk da cewa ruwan sama ya sauka, kuma ya jika duk wadanda suka hallarci taron.
Yanzu dai masu zanga-zangar sun dauki alwashin cigaba dayi har sai anyi wani abu gameda neman daliban mata su sama da 200.