Kowace ranar Allah takaicin iyayen dalibai matan da aka sace a Chibok sai karuwa ya ke yi saboda rashin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki da kuma jita-jita daban-daban da su ke ta ji.
Yau makonni uku kennan da sace dalibai mata su sama da dari biyu daga makarantarsu ta sakandare a garin Cibok dake jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya, a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe.
Yayin da aka share makonni uku da sace dalibai mata a makarantar Sakandare dake Cibok a Jihar Borno, wani dan Majalisar Wakilai ya tabbatar cewa 'yan bindigar sun fara auren 'yan matan.
Yayin da take taron kawo karshen wa'adin shugabannin riko na jihar Sokoto, jam'iyyar APC ta bude taron ne da ta musamman ma daliban da awasu 'yan bindiga suka sace a Chibok dake jihar Borno.
Kusan makonni uku ke nan da wasu 'yan bindiga suka sace dalibai fiye da dari biyu a makarantar 'yan mata dake garin Chibok lamarin da ya tayar da hankanli al'ummar Najeriya gaba daya.
Iyayen ‘yan matan da ‘yan bindiga suka sace a makaranta sun gayawa gwamna ranar litinin cewa sunje neman su a cikin daji,sun kara da cewa har yanzu ba’a ga ‘yan mata dari biyu da talatin da hudu ba,fiye da adadin da gwamnati ta bada. An dauki hotuna 22 Afrilu 2014.
Iyayen dalibai mata fiye da dari biyu da ‘yan bindiga suka sace a makaranta a garin Chibok har yanzu ba’a gansu ba bayan mako daya,duk da kokarin da jami’an tsaro da wasu iyayen yaran suka yi na binsu cikin mugun daji.Wasu daga cikin daliban su tsira da tsalle daga mota ko kuma boyewa a cikin daji.