Mahaifin daya daga cikin yaran da aka sace yace,yana farin ciki ganin hoton bidiyon da ‘yan boko haram suka fito dashi,domin ya ga wata mai kamar ‘yar sa a ciki.
Bai dace ba a koina a duniya ace an sarrafa rayukan yaran mutane wadanda bazu jiba basu gani ba akan rikicin da akeyi.
Daya daga cikin iyayen daliban Chibok ta tabbatar cewa ta ga 'yarta a cikin jerin yaran dake cikin hotunan bidiyon da mutumin dake cewa shine shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar a baya-bayannan.
Bayan wata daya da sace daliban makarantar 'yan mata dake Chibok a kudancin jihar Borno har yanzu shugaban kasar ya kasa ziyarar garin
A wani sabon bidiyo da mutumin da yace shine shugaban kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, ya fitar a baya-bayannan, Abubakar Shekau yace ya musuluntar da wadannan mata, wadanda yace ya sato su, sannan yana bukatar ayi musaya dasu.
Yayin da 'yan jam'iyyar APC suka kaiwa gwamnan jihar Borno gaisuwar jajantawa sabili da daliban Chibok da aka sace gwamna Shettima yace idan sadakar da ransa zai kawo wa al'ummarsa da kasar zaman lafiya to ashirye yake yayi hakan.
Masu zanga-zanga a cikinsu harda tsohuwar Ministan Ilimi, sun jaddada ‘yancinsu na gudanar da taron lumana, yayin da suke kira a dawo da dalibai su sama da 200 da ‘yan bindiga suka sace.
Wasu daga cikin gungun ‘yan mata daliban makarantar sakandaren da ‘yan ta’adda suka kaiwa hari a jihar Bornon Nigeria, sun yi bayanin yadda suka yi sa’ar kubuta daga kangin daga ‘yan Boko haram suka yi wajen shirya kamesu a gidajen kwanansu na makaranta.
Domin Kari