An kama wani mutun mai siyar da katin zabe a jihar Bauchi, a dai-dai wannan lokaci da aka tunkari babban zabe na shekarar 2015 a Najeriya.
Kamar sauran ‘yan Najeriya, shuwagabanni da ‘yan siyasa da ma sauran al-ummomin yankin da hare-haren Boko Haram ya raba da gidajensu a arewacin Jihar Adamawa, sun mayar da martani game da batun dage zabe da aka yi.
A kalla mutane biyar ne aka kashe, biyo bayan fashewar wani Bom a wata kasuwa dake garin Diffa a kudu maso gabashin Nijar Lahadinnan, biyo bayan dakile wani harin Boko Haram akan garin dake bakin iyaka.
Rundunar 'yansandan jihar Adamawa ta bankado wasu bamabamai da aka boye cikin dajin Song
Janaral Buhari ya gayawa magoya bayansa su maida zuciya nesa akan dage zabe da aka yi.
Dabe zabe sabili da halin tsaro tamkar hukumomin tsaron Najeriya sun kunyatar da kasar ne a idanun duniya
Abou Ismaila mazaunin garin Fotokol ya kara haske akan irin ta'asar da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi a Fotokol
Fiye da mutane saba'in ne Boko Haram ta kashe a garin dake kan iyaka da kasar Kamaru
Gwamnatin kasar Chadi ta ce sojojin ta sun kashe yan Boko Haram akalla 200 da suke fada dasu tsakanin Najeriya da Chadi.
Boko Haram sun kai hari garin Fotokol na kasar Kamaru, to amma sojojin Chadi sun fatattake su.
Kwamiti na musamman da Janaral Abdulsalami ke jagoranta yana sa ido ne akan kawar da duk wata dabarar kawo fitina.
Domin Kari