Rikici yayi sanadiyyar kase-kashe a Jahar Filaton Najeria.
Wannan lamarin ya kara tayar da hankalin mutane musamman sabili da alwashin da kungiyar Boko Haram tayi.
Yayinda Janaral Buhari ya kai yakin neman zabe a Maiduguri sai bam ya tashi a wata anguwa.
Gwamnan Damagaran yace a halin yanzu ba sa bukatar sansanin 'yan gudun hijira a garin saboda 'yan uwan wadanda abin ya ritsa da su sun basu mafaka.
Sojojin Nijeriya sun sake kwato sassa dabam-dabam a jiahr Adamawa daga hannun 'yan Boko Haram. Amma har yanzu wasu na shakkar manufar hukumomin Nijeriya game da zaben da ke tafe.
Dakarun Sojojin Najeriya, na samun Nasarar fattakar mayakar kungiyar Boko Haram, a arewacin jihar Adamawa, inda suka kwato kusan dukka kananan hukumomin jihar dake hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
Ansamu nasarar kwato kananan hukumomi shida daga cikin bakwai a jihar Adamawa.
Biyo bayan harin da aka kai a jihar Gombe, gwamnan ya kakabawa wurin dokar ta baci na ba fita dare da rana lamarin da ya zo ma wadanda abun ya shafa bazata.
Muryar Amurka ya samu damar tattauna da mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Namadi Sambo. Ibrahim Alfa Ahmed na Sashen Hausa ya tattauna batutuwa masu nasaba da tsaro da Mr. Sambo, da ma zabe mai zuwa.
Da misalin karfe 12 da wasu dakikoki ne Lahadinnnanm, wata ‘yar kunar bakin wake ta kutsa cikin babbar tashar ababen sufuri dake garin Damaturu, dake Jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya, ta tayar da Bom wanda yayi sanadiyar rayukan mutane 10 da raunata misalin 45.
Asabar dinnan daliban Chibok suka watanni 9 da sacesu da ‘yan bindiga suka yi, abunda yasa kungiyoyin dake hankoron gani an ceto su suke shirin gudanar da wasu hidimomi a birnin Tarayyar Najeriya Abuja.
Domin Kari