Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Bayani Akan Barnar da Mayakan Boko Haram Suka Yi a Fotokol


Jirage masu saukar angulu a Fotokol bayan an fatattaki 'yan Boko Haram
Jirage masu saukar angulu a Fotokol bayan an fatattaki 'yan Boko Haram

Abou Ismaila mazaunin garin Fotokol ya kara haske akan irin ta'asar da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi a Fotokol

Idan ba’a manta ba ‘yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a garin Fotokol dake kan iyaka da Kamaru da Nijar da Najeriya inda suka yiwa mutanen dake sallar asubahi yankan rago kafin hadakar sojojin Kamaru da na Chadi su fatattakesu.

Ga shaidar da Abou Ismaila mazaunin garin da ya tsallake rijiya da baya ranar Laraba biyar ga watan Faburairu, ranar da ‘yan Boko Haram suka kai hari a Fotokol, ya bayar.

Yace “ina Fotokol amma ban san wurin da nake ba. Ina boye domin ina fargaba. Na samu na arce wajejen karfe hudu na safe. Da ma da na tashi raina bai so zuwa masallaci ba domin yin sallar asubahi. Sai na tsayar da shawarar yin salla a gidana. Dana fara jin harbe-harbe na dauka sojojin Chadi ne suke kakkabe ‘yan ta’ada amma bayan ‘yan mintuna kadan sai na soma jin ‘Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu Akbar. Da naji haka nayi zaton karshen rayuwata a duniya ta zo ke nan sai na soma gudu. Suna kamar kafa dari dani sanye da kayan sojoji. Wata bishiya ce ta kare ni na samu na tsira…”

“Sun kawo hari garin ta wurare uku. Sojoji basu yi zaton harin ba domin bayan da dakarun Chadi suka kai hari Gamboru, mayakan suna Narayanan wanda ke da tazarar kilomita tara ko goma. A wannan harin an kashe fararen hula fiye da dari biyu.

Su ma ‘yan Boko Haram da suka halaka gawarwakinsu sun bazu a fili kusa da makaranta dake gaf da sansanin sojoji. Akwai gawarwaki ma baje a kusa da ofishin hukumar kwastan wanda rabinsa an kone. Mayakan Islaman basu kone masallacin ba amma sun kashe duk wadanda suka samu cikin masallatan da suka fi girma guda uku, wato masallacin Imam Mustapha da na Imam Tucharima da na Imam Mahamat Adam wanda suka yanka kamar rago a gaban gidansa. An kone motoci dari da ashirin da takwas tare da gidaje sittin.

XS
SM
MD
LG