Kungiyar Boko Haram dake Najeriya ta kashe mutane fiye da 70 a wani harin da ta kai kan iyaka da kasar Kamaru.
Wata jaridar Kamaru da ake kira Far North Region tace ‘yan Boko Haram sun kai hari akan garin Fotokol da safiyar jiya Laraba inda ta dinga kashe mutane barkatai.
Abafani Mussa wani mazaunin garin ya shaidawa Muryar Amurka Sashen Faransanci cewa mayakan sun shiga wani masallaci inda suka kama yankan wadanda suke yin sallar assubahi kamar raguna.
Musa yace daga bisani kuma sai suka soma bi gida gida suna kashe mutane kafin dakarun Kamaru tare da na Chadi suka tunkaresu. Dakarun kasashen biyu sun samu sun hallaka mayakan da dama yayin da sauran suka arce.
Kasar Chadi tana kan gaban kasashe hudu wurin taimakawa Najeriya domin ta kawar da Boko Haram gaba daya ta kuma sake kwato yankunan da ‘yan ta’adan suka mamaye domin kafa tasu daular akan manufofin irin nasu addinin Islaman.
Tun farko Chadi ta Ambato cewa sojojinta sun fatattaki mayakan Boko Haram daga Fotokol har zuwa garin Gamboru cikin Najeriya ranar Talata. Tayi ikirarin kashe fiye da 200 daga cikin mayakan yayin da ita Chadin ta rasa sojojinta tara