Kwamitin din ne ya shirya taron zaman lumana da aka yi da 'yan takaran shugaban kasa su goma sha hudu inda suka yi yarjejeniyar da suka rabtabawa hannu.
Janaral Abdulsalami Abubakar jagoran kwamitin wanda kuma shi ne ya mikawa farar hula mulki a 1999 ya bada tabbacin kwamitinsa ba zai yi gyangyadi ba kan aikin. Yace shugabannin addini zasu aika masallatai da mijami'u da sakon kada a kashe juna kada kuma ayi barna.
Dangane da barazanar da wasu suka yi cewa idan wanda suke marawa baya bai ci zabe zasu wargaza kasar sai Janaral Abubakar yace babu wanda zai iya wargaza ta. Babu wanda zai yi anfani da 'yancinsa ya taka 'yancin wani. Wadanda ke cewa sama dakasa zasu tashi idan nasu bai ci zabe ba ba abun ji ba ne. Yace sun lura da maganganun kuma sun gayawa 'yan siyasa idan wani yayi furucin banza su fito su musanta.
Mataimakin kakakin kemfen din shugaba Jonathan Yariman Muri yace sun bi wannan shawara sau da kafa. Yace wadanda zasu kyautata masu su ne wadanda suke fadin aikin alherin da Jonathan da Namadi Sambo suka yi.
Haka ma wasu masu marawa bayan wasu gwamnonin PDP na ganin dogaro ga gwamnati kacokan kan kawo tarzomar matasa. Ahmad Kandos yace idan kana siyasa kuma kana da abun yi ba zaka shiga tarzoma ba amma idan ka dogara ga abun da za'a baka kullum ne to dole ka tada tarzoma domin wai ka kare muradun uban gidanka.
Janaral Buhari yace su a cikin lumana suke yakin neman zabe. Ya yiwa magoya bayansa godiya sabili da abubuwan da ya gani a koina ya je cikin kasar.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.