Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Harkokin Wajen Najeriya Da Rasha Sun Tattauna Akan Zaman Lafiyar Yankin Sahel


Yusuf Tuggar da Sergei Lavrov na Russia
Yusuf Tuggar da Sergei Lavrov na Russia

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun tattauna batutuwan da suka shafi moriyar juna da kuma zaman lafiyar yankin a birnin Moscow ranar Laraba.

WASHINGTON, D. C. - A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X wadda a da aka fi sani da Twitter, Tuggar ya ce ganawarsa da Lavrov na kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Najeriya ne, musamman a fannin bunkasar tattalin arziki da samar da zaman lafiyar yankin Sahel.

Yusuf Tuggar
Yusuf Tuggar

“Dangantakar Najeriya da Rasha na da dadadden tarihi, wanda ke da nasaba da hadin gwiwa a fannoni daban-daban da suka hada da diflomasiyya, kasuwanci, da tsaro. A cikin shekarun da suka gabata, kasashenmu sun yi aiki tare a kan batutuwan da suka shafi moriyar juna, tare da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.” Inji Tuggar.

“Ganawar da na yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, na kara karfafa wannan dangantaka ne, musamman a fannin bunkasar tattalin arziki da samun zaman lafiyar yankin.

Sergei Lavrov
Sergei Lavrov

Tattaunawarmu ta mayar da hankali ne kan inganta hadin gwiwa don bunkasa tattalin arziki a Najeriya da tabbatar da zaman lafiya a yammacin Afirka da yankin Sahel."

Tuggar ya kuma ce dage takunkumin da Rasha ta kakaba wa Burkina Faso, Mali da Nijar, ya kara jaddada aniyarta na tallafawa ayyukan tsaro a yankin, ciki har da kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka.

“An kuma amince da muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, tare da yin kira da a kara ba da taimako daga kasar Rasha don magance kalubalen tsaro.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar Da Takwaransa Na Rasha Sergei Lavrov
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar Da Takwaransa Na Rasha Sergei Lavrov

"Wadannan tattaunawa sun yi daidai da manyan manufofin dangantakar da ke tsakanin kasashen Najeriya da Rasha, tare da jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen tinkarar kalubalen da ake fuskanta da kuma inganta ci gaban juna.

"Sun kafa harsashin tuntubar juna a nan gaba da kuma ziyarar da za a iya yi a nan gaba, ciki har da wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai birnin Moscow, wanda ke nuna aniyar kasashen biyu na zurfafa dangantakarsu," in ji ministan na Najeriya.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG