Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya Yayi Kira Da A Gaggauta Kara Shigar Da Agajin Jinkai Cikin Gaza


Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutarres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutarres

Wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da suka hada da Amurka da Birtaniya, sun bukaci a kai karin agajin jinkai ga Falasdinawa farar hula a Gaza ba tare da bata lokaci ba.

Wakilan kwamitin sulhun sun yi gargadin cewa, yanayin jinkai na kara tabarbarewa a yankin.

A halin da ake ciki, Amurka ta gargadi Turkiyya a jiya Litinin akan kada ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar Hamas, tana mai cewa ba za a ci gaba da tafiyar da abubuwa "kamar yadda aka saba" tunda Amurka ta ayyana kungiyar a matsayin ta'addanci.

Rahotanni daga kafafen yada labarai da yawa sun nuna cewa, wasu manyan jami’an kungiyar Hamas da ke wajen Gaza sun je Turkiyya a ‘yan kwanakin nan, bayan da aka nemi su fice daga kasar Qatar.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya ce ba shi da hurumin ya kalubalanci ko musanta wadannan rahotannin, ya ce gwamnatocin da abin ya shafa su zasu yi magana akan inda shugabannin Hamas suke.

Miller ya shaidawa manema labarai a yayin wani jawabin manema labarai a ranar Litinin cewa, bai ga dalilin da zai sa shugabannin irin wadannan miyagun kungiyoyin na ta’addanci za su cigaba da gudanar da rayuwa cikin kwanciyar hankali ba a koma ina ne, hakan ya hada da a manyan biranen daya daga manyan abokan huldar mu.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy yayi kira a gaban Majalisar Dinkin Duniya na a kara yawan tallafi ga Gaza, inda yawan wadanda aka tarwatsa daga mazauna yankin su milyan 2.3 ke cikin mummunan matsalar jin kai.

A wani sakon da aka wallafa ta kafar sadarwar zamani na X, Birtaniya da Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya sunce, kwanaki 400 da aka kwashe a yakin babu wani uzuri ga Isra’ila na haifar da cikas game da shigar da agaji cikin Gaza. Haka ma ba wani uzuri ga Hamas na cigaba da yin garkuwa da mutane. Dole ne a kawo katshen yakin nan—a bude hanyar samar da dawwamanmen zaman lafiya ga kasashen biyu.

Jami’an Amurka sunce suna sa ido kud da kud kan matakan da Isra’ila ke dauka domin inganta halin da Palasdinawa farar hula ke ciki, a yayin da take tattaunawa da Shugabannin Isra’ilan a duk rana.

Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas AGreenfield ta fada a ranar Litinin cewa, a yayin da suke matsa lamba domin ganin an kai ga karshen yakin, dole ne ita ma Isra’ila ta gaggauta daukar karin matakan magance mummunan yanayin jinkan da ake ciki a Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG