Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin G-20 Sun Mayar Da Hankali Kan Sauyin Yanayi


Shugabannin kasashen duniya a taron G20 - Rio de Janeiro, Brazil 2024
Shugabannin kasashen duniya a taron G20 - Rio de Janeiro, Brazil 2024

A yau Talata, shugabannin kasashe 20 mafi karfin arziki a duniya G-20 suka tattauna akan ci gaba mai dorewa da kuma komawa amfani da makamashi mai tsafta.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da suke kokarin kara damammakin samun yarjejeniyar da za su yi amfani da ita wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi a taron Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi dake gudana a kasar Azerbaijan

G20 - Rio de Janeiro
G20 - Rio de Janeiro

Tunda fari, kasar dake karbar bakuncin taron sauyin yanayin mai taken “COP29” ta roki kasashen na G-20 dasu aike da kyakkyawan sako akan bukatar shawo kan matsalar sauyin yanayi tare da samar da ikon da zai taimaka wajen ceto batutuwan da aka tattauna a birnin Baku, na Azerbaijan daga dulmuyewa cikin tabo.

A yayin da duniya ke dosar shekara mafi zafi a tarihi, shugabanni na kokarin su tallafa wajen samar da martanin kasa da kasa akan sauyin yanayi tun gabanin Donald Trump ya sake karbar ragamar shugabancin Amurka a watan Janairu mai zuwa. rahotannin sun ce yana shirye-shiryen rushe manufar Amurka akan dumamar yanayi tare da ficewa daga gagarumar yarjejeniyar nan ta birnin Paris.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya na magana lokacin taron G-20 Rio de Janeiro, Brazil Nuwamba18, 2024
Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya na magana lokacin taron G-20 Rio de Janeiro, Brazil Nuwamba18, 2024

A jiya Litinin, taron Shugabannin G-20 da yanzu haka ke gudana a birnin Rio De Janairo, na kasar Brazil, ya bukaci a samar da sanarwar hadin gwiwa domin “gaggauta kara samarda makudan kudaden yaki da sauyin yanayi daga bilyoyi zuwa tiriliyoyin daloli daga dukkanin hanyoyi” da nufin yin martani ga dumamar yanayi.

Haka kuma sun bukaci masu shiga tsakani a taron COP29 su cimma matsaya akan sabuwar manufar kudade dangane da yawan kudaden da mawadatan kasashe zasu baiwa kasashen masu tasowa domin yakar sauyin yanayi, wannan shine babban jigo a tattaunawar da ake yi akan sauyin yanayin.

Shugaban kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan da Ministan harkokin kasar waje na Rasha Sergey Lavrov suna wata tattaunawa lokacin taron kasashen G20 a Rio de Janeiro, Brazil, Nuwamba 18, 2024.
Shugaban kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan da Ministan harkokin kasar waje na Rasha Sergey Lavrov suna wata tattaunawa lokacin taron kasashen G20 a Rio de Janeiro, Brazil, Nuwamba 18, 2024.

“Shugabannin G-20 sun aike da bayayyanannan sako ga masu shiga tsakani a taron cop29 cewar: kada ku bar birnin Baku ba tare da cimma sabuwar manufa akan samarda kudade ba. hakan wani al’amari ne “daya shafi kowace kasa,” kamar yadda shugaban yaki da sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya Simon Stiell ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Manufar masu shiga tsakani a tattaunawar sauyin yanayin ita ce samar da cikakken daftari akan yarjejeniyar manufar samarda kudade kan nan zuwa yammacin gobe Laraba, a cewar babban mai shiga tsakani a taron yalchin rafiyev na kasar Azerbaijan.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macro, a bayan su Anthony Blinken sakataren harkokin wajen Amurka a taron G-20 Río de Janeiro, Brazil
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macro, a bayan su Anthony Blinken sakataren harkokin wajen Amurka a taron G-20 Río de Janeiro, Brazil

“Mun kara hanzari a tafiyar,” a cewar Rafiyev.” sakamakon zai zamo kyakkyawa kamar jajircewar bangarorin dake cikin yarjejeniyar da za ta taimaka mana wajen samun mafita.”

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG