Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakatar Da Wasu Jami'an Gwamnatin Kaduna Bisa Bayar Da Bayanan Karya


Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

Kotun da’ar ma’aikata ta bayar da umarnin dakatar da wasu manyan jami’an jihar Kaduna guda uku biyo bayan zargen da ake musu na ba da bayanan karya wurin bayyana kadarorinsu, yayin da suke jira su gurfana gaban kotu.

A wata sanarwa da hukumar da’ar ma’aikata (CCB) ta fitar a ranar Alhamis, ta umarci Samuel Peter, kwamishinan tsaro na cikin gida mai riko da Shizzer Bada, kwamishinan kudi da kuma Tijjani Abdullahi, shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jiha, da su sauka daga mukamansu.

Umarnin da aka fitar a ranar 22 ga watan Oktoba, ya biyo bayan karar bangare daya ne da hukumar CCB ta shigar a kotun.

Ana sauraren irin wannan kara a kotu ba tare da bangaren da ake zargi yana nan a kotu ba.

Ana zargin jami’an ne da karya dokar CCB da CCT wadda ta bukaci jami’an gwamnati su bayyana hakikanin kadarorinsu a hukumance daga lokaci zuwa lokaci.

Hukuncin kotun zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a saurari karar da hukumar ta shigar a ranar 21 ga watan Oktoba, tare da tuhume-tuhume kan jami’an.

Sanarwar ta ce kotun ta kuma umurci gwamnan jihar Kaduna da sakataren gwamnatin jihar da su nada ma’aikata na wucin gadi da za su maye gurbin jami’an da aka dakatar da su.

“Kotu ta zartar da wannan hukuncin ne a ranar 22 ga Oktoba, 2024, biyo bayan wata takardar da Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata, wato ‘Code of Conduct Bureau’ a turance, ta gabatar dangane da zargin rashin mutunta dokar da’ar ma’aikata ta, CAP C1 LFN 2004,” in ji Veronica Kato, kakakin hukumar a wata sanarwar.

An shirya jami’an uku za su bayyana a gaban kotun ranar 7 ga watan Nuwamba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG