An soke tafiyar Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima domin wakiltar kasar a taron shugabannin kasashen kungiyar kasashe renon Ingila (Commonwealth), bayan da wani abu ya daki jirginsa a filin saukar jiragen saman JFK dake birnin New York.
Sanarwar da mashawarcin shugaban Najeriya akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar, tace abinda ya daki jirgin ya fasa gilashin gaban direban jirgin.
Shugaba Tinubu ya amince tawagar ministoci ta wakilci Najeriya a taron da zai gudana a Apia, babban birnin Samao, yayin da aka fara aikin gyaran jirgin.
Tawagar, da a yanzu za ta wakilci Najeriya a taron za ta kasance karkashin jagorancin Ministan Muhalli, Balarabe Abbas Lawal.
An samo taron wanda yanzu haka ke gudana a kasar dake tsibirin yankin pacific a rana 21 ga Oktoban da muke ciki, kuma za a kammala shi a gobe 26 ga watan.
Tuni dai Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, suka baro New York zuwa Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna