Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Addinai Sun Gargadi Majalisar Shari'ar Kasa Da Ta Guji Zama Sanadin Kawo Rudani Da Tashin Hankali


Taron Kungiyoyin Adinai
Taron Kungiyoyin Adinai

Kungiyar da ke sasanta tsakanin addinai reshen jihar Filato ta ja hankalin majalisar shari’a ta kasa, a kan ta maida hankali wajen yin nazarin yadda kotunan sauraron kararrakin zabe ke gudanar da shari’u, da a ganinsu ke cike da kurakurai, don kaucewa tashin hankali.

Shugaban kungiyar Interfaith Mediation Center ta jihar Filato a bangaren addinin Kirista, Evangelist Joshu’a Ringsum yace jihar Filato ta sha fama da tashin hankali a baya, don haka suke jan hankalin bangaren shari’a da ya guji zama sanadin haddasa rudani da tashin hankali a jihar.

Shi ma shugaban kungiyar a bangaren addinin musulunci, Imam Othman Abdullahi Ibrahim, yace sun yi aiki tukuru don ganin al’ummar jihar Filato sun fahinci juna, a saboda haka suke gudun duk wani abu da zai maida hannun agogo baya.

Taron Kungiyoyin Adinai
Taron Kungiyoyin Adinai

Barista Isyaku Barau, na Sudan Chambers a birnin Kontagora da ke jihar Neja, yace akwai matsala a harkar shari’a a Najeriya da ke bukatar gyara.

Yayin da kotun daukaka karar zabe ta bukaci a sake gudanar da zabuka na wasu ‘yan majalisun tarayya a Filato ta Arewa, a bangare guda kuwa ta umurci hukumar zabe ta kasa da ta kwace takardar shaidar cin zabe ta dan majalisar wakilai daga kudancin jihar Filato, Isaac Kwallu na jam’iyyar PDP, ta bai wa John Dafan na jam’iyyar APC.

Saurari rahoton Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG