Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Naana Jane Opoku-Agyemang: Mace Ta Farko Da Ta Zama Mataimakiyar Shugaban Ghana


Mataimakiyar Shugaban Ghana
Mataimakiyar Shugaban Ghana

Farfesa Naana Jane Opoku-Agyemang ta zama mace ta farko da babbar jam’iyyar siyasa NDC ta Ghana ta zaba don tsayawa takarar mataimakiyar shugaban kasa.

An tsayar da ita a shekarar 2020, wanda ya kasance wani babban cigaba ga mata, ba kawai a Ghana ba, har ma a nahiyar Afirka baki daya, wajen karfafawa Mata su shiga harkokin shugabanci da siyasa.

An haifi Farfesa Opoku-Agyemang a ranar 22 ga watan Nuwamban 1951, a garin Komenda, yankin tsakiyar Ghana. Ta fara karatunta a makarantar Anglican Girls’ Secondary School, sannan ta kammala a Wesley Girls’ High School, a garin Cape Coast. Daga nan, ta sami digiri na farko a fannin Turanci da Faransanci daga Jami’ar Cape Coast (UCC). Ta ci gaba da samun digiri na biyu da kuma digirin digirgir a fannin Adabi daga York University, Toronto, Canada.

Bayan dawowarta daga Canada, ta fara koyarwa a Jami’ar Cape Coast a matsayin malamar Turanci. Ta kware sosai wajen koyar da adabin Afirka da nazarin jinsi. A shekarar 2008, ta kafa tarihi inda ta zama mace ta farko da aka taba nada a matsayin Mataimakiyar Shugaban Jami’ar UCC (Vice-Chancellor) a Ghana, ta jagoranci jami’ar daga shekarar 2008 zuwa 2012. Wannan nasarar ta bude wani sabon babi a fannin ilimi da shugabanci a Ghana.

Sauye-Sauye a Fannin Ilimi

A matsayinta na Ministar Ilimi (2013-2017), Farfesa Opoku-Agyemang ta aiwatar da manufofi da suka inganta tsarin ilimi a Ghana. Ta fi mayar da hankali kan gina makarantu a yankunan karkara, inganta horar da malamai, da kuma samar da ilimi mai inganci ga kowa, musamman talakawa. Hakazalika, ta yi kokari wajen ganin cewa mata sun sami karin dama a fannin ilimi.

Wadannan matakan da ta dauka sun kara mata farin jini a tsakanin jama’a, inda ake ganin ta zama jagora mai kishin kasa da kuma jajircewa wajen bunkasa al’umma.

Kare Hakkin Mata da Matasa

Bayan rawar da ta taka a fannin ilimi, Farfesa Opoku-Agyemang ta shahara wajen kare hakkin mata da matasa. Ta rika gudanar da tarurruka da gabatar da jawabai kan muhimmancin ilimi da jagoranci ga mata, tana mai cewa mata za su iya cimma duk abin da suke so muddin aka ba su dama da goyon baya.

Wata babbar nasararta ita ce kirkiro tsarin tallafin kudade na musamman domin mata, wanda zai taimaka musu wajen bunkasa harkokin kasuwancinsu. Wannan shirin zai ba wa mata da dama damar dogaro da kansu da kuma habaka tattalin arzikinsu.

Zabinta a matsayin ‘yar takarar mataimakiyar shugaban kasa karkashin tutar jami'iyyar NDC a shekarar 2020 ya kawo karfin gwiwa ga mata da dama.

Kalubale

Kamar kowanne jagora, Farfesa Opoku-Agyemang ta fuskanci kalubale, musamman a fage na siyasa da ya fi zama na maza. Duk da cewa ba ta samu nasara a zaben 2020 ba, takararta ta bude kofar damammaki ga matan Ghana da sauran kasashen Afirka.

Masana siyasa irinsu Mallam Musah K. Dankwa sun bayyana cewa, tana da karfin kawo ci gaba a bangarorin ilimi, tattalin arziki, da kare hakkin mata. Matsayinta a tarihi ya nuna cewa mata za su iya taka muhimmiyar rawa a shugabanci, duk kuwa da irin matsalolin da ake fuskanta.

Farfesa Naana Jane Opoku-Agyemang ta zama alamar canji da ci gaba a Ghana da Afirka baki daya. Ko da kuwa ace jami'iyyar ta ba suyi nasara ba a zaben 2024 a Ghana, ta kafa tarihi da ta nuna cewa mata za su iya jagorantar al’umma da yin nasara. Ita ce wani misali na yadda shugabanci ya kamata ya kasance da gaskiya, jajircewa, da kishin kasa.

A matsayin wata jaruma mai kishin kasa, sunanta zai ci gaba da zama a jerin mata gwaraza da suka taka rawar gani wajen gina al’umma.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Abdulkarim:

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:06 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG