A jiya Alhamis Amurka tayi bikin ranar samun 'yancin kai na tsawon kusan karni biyu da rabi, hutun ranar 4 ga watan Yuli da ta kasance ranar da ta ayyana cin gashin kanta daga Birtaniya.
Hukumar da ke sa ido kan kafafen yada labarai na Radio da Talbijin ta Kasar Turkiyya RTUK ta kwace lasisin wata tashar Radio mai zaman kanta a ranar Laraba, sakamakon barin baki game da kisan kiyashin da aka yi a Armenia, a tashar.
Karin tashe tashen hankulla ya kara Kamari ne a karshen watan Fabrairu, bayan dimbin jerin shiryayyun hare hare kan muhimman gine ginen gwamnati da sannu a hankali ya kai ga Priministan kasar Ariel Henry ya tattara shugabancin kasar ya ajiye a watan Apirilu.
Shugaba Ruto dai na fuskantar rikici mafi muni tun bayan da ya kama aiki a shekarar 2022, inda wasu masu zanga zangar ke kiran ya sauka daga shugabancin kasan, suna mai zargin shi da rashin iya mulki.
Jam’iyun adawa na Faransa sun kulla wata yarjejeniya cikin sauri domin kokarin kange nasarar kud da kud ga yar jam’iya mai ra’ayin rikau, Marine Le Pen.
Shugaban Amurka Joe Biden ya fada cikin wata sanarwa cewa, al’ummar Haiti sun cancanci zama lafiya a gidajen su, su gina ingantacciyar rayuwa ga iyalan su, su kuma more yancin demokradiyya
Wakilan Sudan sun zargi Hadaddiyar daular larabawa da taimaka wa dakarun RSF ta hannun mayakan sa-kai dake Chadi, kudancin Libya da kuma birnin Khartoum.
A yau Talata ake sa ran Shugaban Amurka Joe Biden zai sanar da wani gagarumin sabon shirin da zai kawar da barazanar mayar da dubban mutanen da suka auri yan kasar Amurka zuwa gida.
A ranar Alhamis bankin duniya ya sanar da amincewa da ba Najeriya bashin zunzurutun kudi har dala biliyan 2.25 domin taimaka mata daidaita tattalin arzikinta, biyo bayan sauye sauyen da ta yi da kuma fadada kokarin tallafa wa marasa karfi.
A ranar Alhamis kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya zarta da kudurin da ya nemi dakarun kar ta kwana na Sudan da su gaggauta daina kawanyar da su ke yi a babban birni daya tilo a yankin Arewacin Dafur da ba ta da iko da shi, kuma wurin da aka ruwaito cewa mutane sama da miliyan suka fake.
A ranar Lahadi ne masu kada kuri’a a kasar Mexico su ka je rumfunan zabe domin zaben sabon shugaban kasa, da ake shirin ganin abin mamaki.
Domin Kari