Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Shirye Shiryen Mika Mulki Ga Sabuwar Gwamnati A Amurka


Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump
Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump

A yayin da zababben shugaban Amurka ke shirye shiryen kama aiki, wani ingantaccen tsari na tafe na ganin an mika mulki daga gwamnati mai barin gado zuwa ga sabuwar gwamnati mai kamawa cikin kwanciyar hankali.

A yayin da zababben shugaban Amurka ke shirye shiryen kama aiki, wani ingantaccen tsari na tafe na ganin an mika mulki daga gwamnati mai barin gado zuwa ga sabuwar gwamnati mai kamawa cikin kwanciyar hankali.

Kwamitin mika mulkin, yace akwai kyakkyawan tsarin da ake kai na ganin an mika mulki ga zababben shugaba Donald Trum cikin girma da arziki.

Mika mulki cikin kwanciyar hankali, ingantacciyar al’ada cike da alkawari, kuma muhimmin bangare na democradiyyar Amurka.

A duk lokacin da aka kammala zaben shugaban kasa a Amurka, akan yi shirye shirye da hada hada iri dabam dabam kafin a rantsar da sabon shugaba ko sabuwar shugaban kasa domin kama aiki.

Ana iya ganin kwanaki 76 daga zabe zuwa bikin rantsarwa wani dogon lokaci mai tsawo, to amma a zahiri, sauya gwamnati daga wata zuwa wata abu ne mai sauki, cewar Michael Shurkin, wanda yayi aiki a kwamitin tsaron kasa, wanda a yanzu shine, daraktan shirye shirye a wani kamfanin bayar da shawarwari kan kasuwanci da muhimman tsare tsare na 14 North Strategies.

Muna son tabbatar da ganin shugaban kasar yayi nasara.Don haka idan suna son sauya manufofi, zamu basu hadin kan yin haka, ta hanyar sanar da su duk abinda muka sani, mu kuma bayyana musu abinda ake ciki.

Zababben shugaban kasar ba zai shiga ofis ba har sai ranar 29 ga watan Janairu, to amma dole ne a soma shirye shirye tun kafin ranar, cewar Valerie Smith Boyd na cibiyar shirye shiryen mika mulki ga shugaban kasa.

Ya cigaba da cewa, aiki ne babba, kuma abu na farko da hukumar mu ta yi shine, kokarin bayar da kwarin guiwa gay an takarar shugaban kasa, kan su fara shirya tsare tsaren su tun kafin zabe. An sani cewa, hankalin su zai fi karkata ne ga neman yin nasara a zabe, to amma duk da haka akwai bukatar ganin sun nada kungiyoyi dabam dabam da zasu duba cancantar dubban daruruwa domin zabo mutanen da suka dace wajen taimaka mu su cika alkawurran da suka dauka.

Boyd yace, cika gurabai a mukaman gwamnati ba karamin aiki bane. Da dama daga cikin mukaman na bukatar amincewar majalisar Dattijai, yayin da dole ne saura su fuskanci tantancewar tsaro, wanda hakan ka iya daukar lokaci.

Ya kara da cewa, ‘’muna kallon lokacin mika mulkin a matsayin lokaci mai tsammatsi ga kasa, saboda wadanda za’a nada a mukaman siyasa, manyan shugabanni na barin wata gwamnati. Ana iya samun tsaiko wajen shugowar sabbin jami’ai, wand aba shakka hakan na iya zuwa da kalubale a tattaunawa tsakanin juna ko fahimtar dokoki da nauye nauye.

Amurka dai na da dogon tsayayyen tarihi bisa al’ada na mika mulki cikin kwanciyar hankali, kama daga, farko a shekarar 1797, lokacin da George Washington ya mika shugabancin kasa ga John Adams, wani mika mulki da ya gudana cikin nasara, da

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG