Isra’ila tace ta hallaka jagoran Hezbollah Sayyed Hassan Nasrallah a yayin wani hari ta sama da ta kai kan hedikwatar kungiyar dake birnin Beirut na kasar Lebanon. Kungiyar Hezbollah ta tabbatar da labarin mutuwar.
A karon farko cikin gwamman shekaru, al'ummar Jammu da Kashmir na Indiya sun fita rumfunan zabe inda su ka zabi yan'majalisun dokoki da za su wakilce su.
DANDALIN YAN JARIDA: Tattauna Batun Ambaliyar Ruwa A Yankin Arewa Mai Nisa Da Karancin Wutar Lantarki A Kasar Kamaru, Satumba, 22, 2024
A yau Asabar ake yin zaben kujerar gwamna a jihar Edo da ke yankin Niger Delta a Najeriya cikin tsauraran matakan tsaro, ko da yake, jama'a basu fita zaben ba sosai saboda kalubalen tsaro.
Wasu fitattun malaman addinin Islama daga Najeriya sun yi kira ga 'yan Afrika mazauna Turai da suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin sauraran wa’azi daga bakin maluman a taron da aka saba gudanarwa shekara-shekara a Turai a kan muhimmancin zamantakewa mai kyau.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta bayyana cewa har yanzu ba a kai ga tantance yawan rayukan da aka yi asara ba, a dalilin ambaliyar ruwan da ta faru a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Domin Kari