Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yuwuwa A Mika Rahoton kwamitin Da’ar Majalisa Kan Matt Gaetz Ga Kwamitin Da Zai Tantance Shi A Majalisar Dattijan Amurka


Matt Gaetz
Matt Gaetz

Ana sa ran kwamitin ladabtarwa na Majalisar Wakilan Amurka zai gana gobe Laraba domin yanke shawara kan ko ya fitar da rahoton bincikensa kan tsohon dan majalisa Matt Gaetz ko a’a.

Ana zargin Matt Gaetz da yin lalata da kuma amfani da miyagun kwayoyi, kafin Shugaban kasa mai jiran gado Donald Trump ya zabe shi don zama babban lauyan kasar a sabuwar gwamnatinsa.

Sanatocin Amurka da yawa ‘yan Democrat da na Republican, na neman a fitar da rahoton domin duba cikakken bayani akan Gaetz, yayin da suke sauke nauyin da ya rataya a wuyansu bisa ga kundin tsarin mulki na tabbatar da, ko kin amincewa da wanda sabon Shugaban kasa ya zaba a Majalisar Ministocinsa.

A ranar Larabar da ta gabata ne Trump ya zabi Gaetz mai shekaru 42, dake wakiltar jihar Florida a karkashin jam’iyyar Republican, wanda ya kwashe shekaru 8 a matsayin dan majalisa, don zama babban jami’i a hukumar shari’ar kasar. ‘Yan sa'o'i kadan bayan nadin, Gaetz ya yi murabus daga Majalisa, duk da cewa an sake zaben shi don wa'adi karo na 5. Murabus din da yayi ya kawo karshen binciken da kwamitin ladabtarwar Majalisar ke yi, wanda ya kusa kammalawa.

To sai dai ba a tabbatar da ko kwamitin binciken zai cigaba ya bayyana matsayar da ya cimma ba.

Kwamitin mai 'yan Democrat biyar da 'yan Republican biyar, ya rika bin diddigin zarge- zargen da ake yi wa Gaetz na yin lalata da wata yarinya yar shekara 17 da haihuwa, da yin tu’ammali da miyagun kwayoyi. Gaetz ya karyata zarge zargen. Bangaren shari’a, da Gaetz din ke sa ran jagoranta, ya binciki batun, to amma tun a bara, yaki ya gabatar da tuhuma a kan sa.

Kakakin Majalisa Mike Johnson wanda ke jagorantar dan rinjayen da Republican ke da shi a Majalisa, ya yi turjiya kan bayyanar da rahoton kwamintin da’ar, saboda Gaetz a yanzu ba dan majalisar ba ne. Duk da dai a can baya an samu lokutan da aka yi hakan.

Johnson ya shaidawa kafar CNN a ranar Lahadi cewa, sanatocin dake duba zaben da aka yiwa Gaetz a matsayin babban jami’in shari’ar kasar, zasu yi gagarumin aikin tantancewa, kuma basa bukatar ganin rahoton kwamitin da’a na Majalisar. Wasu sanatocin na tunanin mika goron gayyata muddin ba’a gabatar masu da rahoton ba.

Sanatan Republican Markwayne Mullin ya shaidawa Shirin Meet the Press, na kafar NBC cewa, ya kamata kwamitin binciken ya mika rahoton ga Majalisar dattijai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG