Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Zai Kara Harajin Kashi 25% kan Kasashen Mexico Da Canada


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Dukkan manyan kasuwannin hannayen jarin Amurka uku sun fadi sosai a kusan karshen hada-hadar jiya yayin da Trump ya yi wannan sanarwa.

Shugaba Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa, zai sanya sabon haraji na kashi 25% da zai fara aiki da tsakar daren yau kan kayyakin da ake shigowa da su daga manyan abokanan kasuwancin Amurka biyu, kasashen Mexico da Canada, inda ya yi watsi da shaidar cewa kasashen makwabta sun dakile kaura ba bisa ka’ida ba da kwararowar muggan kwayoyi zuwa cikin Amurka kamar yadda ya bukaci.

“Harajin, kun sani, an kammala shirya su,” Trump ya fada a fadar White House. “Za su fara aiki daga gobe.”

Dukkan manyan kasuwannin hannayen jarin Amurka uku sun fadi sosai a kusan karshen hada-hadar jiya yayin da Trump ya yi wannan sanarwa.

Sakamakon karin kudin fito na iya durkusar da tattalin arzikin kasashen uku, tare da yiwuwar rage bukatar kayayyakin Amurka daga Mexico da Canada wanda za su kara tsada ga masu sayayya da kasuwancin Amurka na kayayyaki da a zahiri ake jigilar su zuwa Amurka.

A nan take dai ba a fayyace yadda Mexico da Canada za su maida martini ba, to amma da shugabar Mexicon Claudia Sheinbaum da Firai Ministan Canada Justin Trudeau duk sun yi barazanar kara nasu harajin akan kayan da ake fitarwa zuwa Amurka, muddin Trump ya yi nasa karin.

Shugaban na Amurka ne ya fara sanar da karin kashi 25% a wata gudan da ya gabata, inda ya yi ikirarin cewa, Canada da Mexico basa yin abin da ya dace wajen taka birki ga masu shiga Amurka ba bisa ka’ida ba da kuma kwararar miyagun kwayoyi zuwa cikin Amurka, musamman muguwar kwayar nan ta opioid fentanyl.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG