Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan Burtaniya Zai Ziyarci Trump Kan Ukraine


Firai Ministan na Burtaniya, Keir Starmer
Firai Ministan na Burtaniya, Keir Starmer

Starmer zai yi kokarin jarraba kasadar diflomasiya ta hanyar ba da kariya ga mahukuntan birnin Kyiv ba tare da ya fusata Trump ba, wanda tattaunawarsa da gwamnatin Shugaba Vladimir Putin na Rasha ta baiwa Turai matukar mamaki.

Shugaban Burtaniya Keir Starmer zai kai wata ziyara mai cike da kasada zuwa fadar White House a Alhamis mai zuwa domin yunkurin gamsar da takwaransa na Amurka Donald Trump ya dauki alkawarin bada kariya ga kasar ukraine a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta da rasha.

Firai Ministan na Burtaniya zai nemi ya dora a kan ziyarar da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ya kai birnin Washington a jiya Litinin.

Sai dai shugaban na Faransa yace tattaunawarsa da Trump a kan cikar shekaru 3 da mamayar Rasha a Ukraine ta nuna cewa akwai mafita duk da fargabar da ake da ita ta samun baraka tsakanin kasashen.

A nasa bangaren Starmer zai yi kokarin jarraba kasadar diflomasiya ta hanyar ba da kariya ga mahukuntan birnin Kyiv ba tare da ya fusata Trump ba, wanda tattaunawarsa da gwamnatin Shugaba Vladimir Putin na Rasha ta baiwa Turai matukar mamaki.

Manya a cikin muradan Starmer su ne samun tabbaci daga Trump na cewa Amurka za ta samar da abin da ake kira da kariya daga hare-hare ta sama da musayar bayanan sirri da safarar kayayyakin bukatun soja domin tallafa wa dakarun Turai din da za’a tura Ukraine domin sa idanu akan tsagaita wuta.

Mahukunta biranen London da Paris ne ke jagorantar shirin tura “rundunar kawar da fargaba” ta akalla sojoji 30, 000 domin ba da kariya ga Ukraine bayan karewar yaki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG