Shugabar kasar Mexico, Claudia Sheinbaum tace tana fatan tattaunawa da shugaban Amurka Donald Trump akan batun haraji.
A yau Alhamis Trump yace zai kakaba karin kaso 10 cikin 100 na haraji akan kayyakin China da ake shigarwa kasarsa yayin da a mako mai zuwa zai cigaba da shirinsa na kakaba haraji akan kayayyakin kasashen Canada da Mexico, inda ya ba da misali da fasakwabrin kwayar Fentanyl wacce yace ba “za a lamunta ba.”
Tunda fari Trump ya sanar - amma ya dakatar daga bisani - da batun kakaba harajin kaso 25 cikin 100 a kan kayayyakin da ake shigowa da su Amurka daga kasashen Canada da Mexico a watan da muke ciki sakamakon matsalar bakin haure da muguwar kwayar nan ta Fentanyl, inda za a sassauta a kan makamashin da ake shigowa da shi daga canada.
Sai dai dakatarwar ta tsawon wata guda za ta kare a Talata mai zuwa.
Biyo bayan tambayar manema labarai akan ko yana shirin cigaba da aiwatar da batun kakaba harajin a mako mai zuwa, Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a yau Alhamis cewa matukar ba’a dakatar ko takaita matsalar fataucin kwayar Fentanyl ba, batun kakaba harajin da yake shirin zai wakana kamar yadda aka tsara.
“Haka kuma za a caji China karin harajin kaso 10 cikin 100 a wannan rana,” a cewar Trump.
Dandalin Mu Tattauna