Ana sa ran yakin Rasha da Ukraine ya mamaye jawabin Trump dangane da rawar da gwamnatinsa ke takawa wajen shiga tsakani a tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin dake rikici da juna.
Akwai yiyuwar shugaban Amurkan ya yiwa majalisar karin haske akan matsayarsa game da yakin Isra'ila da kungiyar Hamas da kuma makomar Gaza.
Yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakaninsa da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyehu a ranar 4 ga watan Fabrairun da ya gabata, Trump ya kawo shawarar mayar da zirin Gaza zuwa abin da aka ruwaito shi yana cewar "dausayin yawon bude idanu na gabas ta tsakiya."
"Amurka za ta karbe iko da zirin tare da gina shi da samar da dimbin guraben aikin yi da za su samar da wuri mai kasaita", inji Trump
Haka kuma Trump zai yi tsokaci a kan irin sukar da ake yiwa gwamnatinsa a bisa kokarinta na rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa da kuma takaita zamba da barna.
An zabi Sanata Elissa Slotkin, tsohon mai yiwa hukumar leken asirin Amurka, CIA, fashin baki domin yin martani ga jawabin Shugaba Trump daga bangaren 'yan jam'iyyar Democrats masu adawa.
Me yiyuwa Amurkawa su bibiyi martanin Sanata Slotkins da cikakken jawabin Trump galibi kai tsaye ta na'urar intanet ko shafukan sada zumunta a daren yau Talata ko kuma su karanta sharhinsu a washegari Laraba
Dandalin Mu Tattauna