Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ganawar Trump Da Zelensky Dangane Da Yarjejeniyar Ma'adinai Ta Katse Babu Shiri


Shugabanin Amurka da Ukraine sun gaza cimma matsaya game da yarjejeniyar ma'adinai yayin da zukata suka hasala game da mamayar Rasha da kuma makomar tattaunawar.

A yau Juma'a Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky suka yi musayar yawu da cacar bakin da ba'a taba ganin irinta ba a ofishin Shugaban Amurka, al'amarin da ya jefa kokarin da aka yi na kawo karshen yaki da Rasha cikin garari.

"Ko dai ka kulla yarjejeniya ko kuma akasin hakan," Trump ya shaidawa Zelensky cikin fushi, yayin da ganawar da ake nufin ta sassauta zukata game da tuntubar bazatar da Amurka ta yiwaRasha ta kare da kara harzukasu.

"Kana wasa da rayukan miliyoyin mutane. Kana kokarin takalo yakin duniya na 3 kuma wannan abinda da kake yi cin mutuncin ne ga kasar nan" a cewar Trump.

Zelensky ya isa fadar White House ne da nufin rattaba hannu akan yarjejeniyar musayar ma'adinan Ukraine da tattaunawar zaman lafiya da Rasha, duk da cewar a baya bayan nan Trump kira takwaransa na ukraine da mai mulkin kama karya.

Ganawar na zuwa ne bayan yunkurin diflomasiyar da ya tilasta shugabanin Faransa da Burtaniya zuwa fadar White House domin shawo kan Trump kada ya juyawa Kyiv baya.

Sai dai zukata sun hasala bayan da Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance yace ana bukatar diflomasiya domin kawo karshen yakin. Zelensky ya tambayi wacce irin diflomasiya ake nufin daga nan sai Vance ya zarge shi da nuna rashin mutuntawa a cikin ofishin Shugaban Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG