A shirye Ukraine take ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar hakar ma'adinai da Amurka, kamar yadda Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya shaidawa manema labaran Burtaniya a jiya Lahadi.
"Za'a rattaba hannu a kan yarjejeniyar da ke bisa tebur matukar bangarorin 2 sun shirya," kamar yadda ya shaida a hirarsa da wasu manema labaran Burtaniya ta tsakar dare bayan wani gagarumin taro da yayi a birnin London.
Yarjejeniyar wacce ya kamata ta zama matakin da zai taimaka wajen kawo karshen yakin Ukraine ta cije bayan wata arangama da Shugaba Donald Trump na Amurka a fadarsa wacce kafofin talabijin suka yada.
"Idan muka amince mu rattaba hannu a kan yarjejeniyar ma'adinan, mu a shirye muke muyi hakan."
Zelensky ya yi balaguro zuwa Amurka da gudanar da cikakkiyar ziyara a fadar White House a Juma'ar da ta gabata domin rattaba hannu a kan yarjejeniyar ma'adinai tsakanin Amurka da Ukraine da nufin gudanar da aikin hadin gwiwa na hakar dimbin ma'adinan da Ukraine din keda shi, a wani bangare na aikin farfadowa daga yaki a yarjejeniyar sulhun da Amurka ta shiga tsakani.
Dandalin Mu Tattauna