Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump na jam'iyyar Republican ya sake kunna sabuwar wutar kace-nace


Donald Trump na jam'iyyar Republican mai neman jam'iyyarsa ta tsayar dashi takarar kujerar shugaban kasa
Donald Trump na jam'iyyar Republican mai neman jam'iyyarsa ta tsayar dashi takarar kujerar shugaban kasa

Dan takarar jam’iyyar Republican na sahun gaba Donald Trump, ya kunno wutar kace-nace tare da kusheshi game da yadda ya bayyanawa jama’a cewa, zai hukunta matan da suka zubar da ciki idan aka haramta hakan a Amurka.

Sa’o’i kadan bayan ya sha caccaka daga mutane, sai ya lashe amansa a wata takardar sanarwa da ya fitar cewa, hukuncin da zai yi zai shafi wadanda suka yi likitancin zubar da cikin ne kawai ba masu cikin ba.

Inda ya kara da cewa, ita wadda aka zubarwa cikin ta fada hatsarin wadanda suka aikata din ne daga ita har abinda ke cikinta. Wannan ikirarin na hukunta wacce ta zubar da ciki ya fito ne a lokacin hirarsa da gidan talbijin na MSNBC.

Babban abokin hamayyarsa Ted Crus kuwa cewa yayi, Trump na ukatar sanin ilimin yadda ake siyasa. Sannan hakan ya nuna Donald ba shi da zuzzurfan sanin al’amuran al’umma na yau da kullum.

Ted ya kara da cewa, Trump na iya furta kowace irin kalma don kawai ya ja hankulan jama’a. sai dai shima Ted Cruz da dan takara John Kasich suna adawa da ‘yancin zubar da ciki.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG