Inda ko wane dan takara ke fatan cinye duk jihar da ake zaben a jam’iyyarsa. Sanatan jihar Texas kuma daya daga ‘yan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar Republican wato Ted Cruz, yana samun nasara a zaben jam’iyyar na fidda gwani a jihohi irin su Kansas da Maine.
Shi ma Trump yana samun nasara a irin su Louisiana da Kentucky. Shi kuma Sanata Bernie Sandars, yana samun nasara akan Hillary Clinton ta jam’iyyarsu ta Democrat a jihohi kamar Kansas da Nebraska, ita kuma Hillary din na tsere masa a irin su Louisiana.
Ana dai wannan zabuka ne a jihohi guda 4 hade da wani yankin Amurka mai cin gashin kansa wato Puerto Rico da ke tsibirin Caribbean. Zabukan zasu gudana daga jiya Asabar ne har zuwa yau Lahadi.
Wannan tseren kuri’un kwatar kai, yana daga cikin wadanda ke da matukar tasiri in dan takarar ya yi nasara. Wanda a karshe dai jam'iyyun guda biyu zasu fidda mutum daya da zai wakilci kowacce a takarar shugabancin Amurka.