Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat da Donald Trump na jam’iyyar Republican sun kara jaddada matsayinsu na ja-gaba a kokarin neman zamowa ‘yan takarar shugaban kasar Amurka na jam’iyyunsu, a bayan da suka samu manyan nasarori a wasu muhimman jihohin da suka jefa kuri’un tsayar da ‘yan takara jiya talata, ranar da ta fi kowacce muhimmanci a kakar tsayar da ‘yan takara a Amurka.
Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Clinton ta lashe jihohin Tennessee, Alabama, Georgia, Virginia, Arkansas, Texas da kuma Massachusetts. Shi kuma abokin hamayyarta a jam’iyyar ta Democrat, Bernie Sanders mai ra’ayin gurguzu, ya lashe jihohin Vermont, Oklahoma, Minnesota da Colorado.
A bangaren ‘yan jam’iyyar Republican kuma, Trump ne ya lashe jihohin Arkansas, Tennessee, Georgia, Alabama, Virginia, Vermont, da Massachusetts. Shi kuma sanata Ted Cruz ya sami nasara a jihohin Texas da Oklahoma da Alaska, sanata Marco Rubio shi kuma ya sami nasararsa ta farko a jihar Minnesota.
Wanna sakamakon bai zo da mamaki ba. Saboda zaben jin ra’ayi da aka yi ya nuna cewa Trump da Clinton su za su yi kan gaba a zaben na jiya Talata.