Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya na cikin hadari idan Trump ya samu shugabancin Amurka


Donald Trump na jam'iyyar Republican dake neman shugabancin Amurka
Donald Trump na jam'iyyar Republican dake neman shugabancin Amurka

Duniya zata shiga wani halin rudanin tattalin arziki da karfafawa 'yan ta'ada irin su ISIS dake ikirarin kafa daular Islama idan har Donald Trump ya zama shugaban kasar Amurka

Wata kungiya mai gudanar da bincike karkashin mujjalar The Economist da ake kira da turanci ECONOMIC INTILLIGENT UNIT dake kasar Birtaniya ta bayyana kasancewar dan Takaran shugaban kasar Amurka a karkashin tutar Jamiyyar Republican Donald Trump a matsayin wata babbar barazana ta 6 daka iya fuskantar duniya.

Wanda aka alakanta shi da ta'adanci da kuma lalata tattalin arzikin duniya.

A cikin jerin wadanda kungiyar ta zayyana a matsayin wadanda suke da hadari a duniya sun hada da tattalin arzikin kasar China da ka iya tafiyar hawainiya a matsayin na farko sai kuma rawar da kasar Rasha ta taka a Syria da Ukraine wanda wannan ya haifar da yakin cacar baki, sai batun bashi dake da nasaba da wasu kasuwannin duniya, kana akwai batun rudanin da ya kunno kai a cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Sai dai kungiyar tace bata sa ran Donald Trump yayi nasara a zaben na watan Nuwamba amma kuma alamu na nuna cewa yana iya samun nasara wanda tace idan hakan ya faru to akwai hatsari.

Wasu daga cikin hujjojin da kungoiyoyin ta kafa ko sune yadda yake sukan batun kasuwanci bada tsangwama ba, tare da ganin an kashe ‘yan uwan wadanda aka samu da hannu a duk abinda ya shafi ta'addanci, sai kuma batun mara wa wata kungiyar kasar Syria baya.

XS
SM
MD
LG