Trump ya ba takwarorin sa rata mai yawa a kan sauran mutane biyu da suka rage cikin masu adawa da shi a wannan yunkurin, yayin da a bangaren ‘yan Democrat kuma, ratar da ke tsakanin tsohuwar sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton da sanata Bernie Sanders ta ragu.
Wannan kuri’ar ta NBC News/Survey Monkey da aka fitar yau talata, ta nuna cewa attajiri Trump, mai kaifin harshe, yana samun goyon baya daga kashi 48 cikin 100 na ‘yan jam’iyyar Republican, nesa sosai da sanata Ted Cruz daga Jihar Texas, mai tsananin ra’ayin rikau wanda ke da goyon bayan kashi 27 cikin 100. Gwamna John Kasich na Jihar Ohio yana matsayi na uku da kashi 18 cikin 100.
Har'ila yau, Trump yana da wakilai fiye da duk sauran ‘yan takarar a zauren babban taron tabbatar da dan takarar shugaban kasa da za a yi cikin watan Yuli. Sai dai ba a tabbatar da ko Trump zai iya samun rinjayen wakilai masu tsayar da dan takarar kafin lokacin wannan taron ba.
A bangaren ‘yan Democrat, Clinton tana samun goyon bayan kashi 49 cikin 100 yayin da Sanders yake samun goyon bayan kashi 43 cikin 100.