‘Yan takarar da suke kan gaba a zaben fidda gwani na jamiyyun siyasar nan guda biyu Republican da Democrat na Amurka sun raba kuriun su tsakanin su da wadanda suke abokan karawar su a jiya talata, a jihohin yammacin Amurka.
Dan Takararar jamiyyar Republican Donald Trump ya samu nasarar lashe zaben Arizona da daukacin duka wakilai 58, inda ya doke abokin karawar sa Ted Cruz da wurin ratan kashi 20.
Sai dai kuma Cruz ya yunkuro a inda ya samu nasara a Utah, domin ko ya samu sama da rabin kuriun da aka jefa, wanda wannan ya bashi damar samun daukaci kuriu 40 din da aka kada a wannan wurin, wanda hakan yahana wa Trump koda kwaya daya daga ciki.
Yanzu haka dai Cruz da sauran ‘yan takaran na Republican wato gwamnan jihar Ohio John Kasich suna kokarin ganin sun hana shi Trump samun kuriar wakilai 1,237 wadda sune zasu bashi damar samun nasarar rikewa jamiyyar tuta.
A bangaren jamiyyar Democrat ko Sanata Berni Sanders ya samu nasara har sau ninki biyu, inda ya lashe kuri'un gaggan ‘yan jamiyyar a Idaho da kuma Utah da wajen kashi 70 fiye da Hilary.
Sai dai ‘yan jamiyyar democrat sun raba kuriaar su kusa dai-dai wadaida, wanda hakan yasa dole sai Sanders samu kuriu masu yawan gaske domin ganin yakai ga cimma ita Hilary .
Ita dai yanzu haka ta lashe zaben da akay a Arizona kuma ta bashi babban tazara a wannan zaben