'Yan takara dake neman shugabancin Amurka suna musayan yawu akan yadda zasu kawar da barazanar ta'adanci biyo bayan hare-haren da aka kai kan birnin Brussels dake Belgium.
Hamshakin attajirin nan dake neman jam'iyyarsa ta tsayar dashi takarar shugaban kasa Donald Trump yace harin Brussels a kasar Belgium da ya hallaka mutane 31 tare da jikata wasu 271 da bai faru ba inda mahukuntar kasar sun yi anfani azabtarwa da ukuba wa Salah Abdeslam wanda ya jagoranci harin da aka kai Paris amma kuma aka cafkeshi makon jiya.
Da aka kamashi an ce yana magana tare da bada wasu bayanai amma Trump yace jnda an gana mashi azaba da ya yi magana da wuri tare da fasa kwai.
Shi ma mai fafatawa da Trump Ted Cruz yace kasar ta daina karban 'yan gudun hijira daga kasashen dake da 'yan kungiyar al-Qaida da dama da kuma mayakan jihadi na kungiyar ISIS. Ya bukaci mahukuntan Amurka su ba 'yansanda ikon yin sintiri a wuraren da musulmai suka fi yawa a koina cikin kasar.
Ita ma 'yar takara a karashin jam'iyyar Democrats tace bama gina katanga ko kuma mu juyawa kawayenmu baya. Ba zamu yi watsi da abubuwan dake aiki ba da wadanda basa aiki mu soma ganawa mutane azaba, inji Hillary Clinton