Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, yayi tur da gungun masu zanga zanga kan gangamin yakin neman zabe da ya so yi a Chicago ranar jumma'a, yana cewa "abun kunya ne" kuma yace 'shiri ne," amma abokan takararsa sun fada yau Asabar cewa, lafazin da Trump yake amfani da shi a yakin neman zabensa shine ya janyo arangamar da ta auku.
Trump yace, masu zanga zangar ne suka kuntatawa magoya bayansa da matsin lamba, a arangamar data auku a daren jiya a jihar Illinois, al'amari da yace "kwararru ne suka kitsa lamarin."
"Tilas ne mu maida martani," inji Trump.
A wani gangamin yakin neman zaben da ya gudanar Asabar din nan a jihar Ohio, hamshakin dan kasuwan, ya gayawa gungun magoya bayansa cewa, yana kira ga dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Democrat Bernie Sanders, ya gayawa magoya bayansa su daina abunda suke yi.
Ahalinda ake ciki kuma,'yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton, tayi Allah wadai da kalaman mutumin da yake kan gaba a takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, kan abunda ta kira "kalmai masu "hadari," tayi kira ga masu zabe, su tashi tsaye wajen magance wannan "nuna fin karfi, da muzurai da nuna kyama," bayan arangama data auku a daren jiya a birnin Chicago, a wurin taron Donald Trump.