Dan takararar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump yana aza laifin kassara gangamin siyasarsa a birnin Chicago ranar Jumma'a, kan dan takarar shugaban kasa, karkashin jam'iyyar Democrat, Bernie Sanders da magoya baynsa, al'amari da ya tilasta soke gangamin.
Fada ya barke tsakanin magoya bayan Donald Trump da da masu adawa da shi, kamin yansanda su tarwatsa gungun jama'an, suka kama mutane biyar.Da dama daga cikin masu zanga zanga a dandalin taron suna ta kiran sunan "Bernie Bernie," suna kuma kada alamomin yakin neman zabensa.
Senata Sanderas ya fitar sanarwa jiya Asabar, ya musanta zargin cewa kwamitin yakin neman zabensa ne ya shirya zanga zangar, ya aza laifin akan lafain da Trump yake amfani da shi a yakin neman zaben ne ya haddasa arangamar.
Sanarwar tace "abunda ya janyo tarzoma a gangamin yakin neman zaben Trump shine dan takarar da yake karfafa wariya da banbanci kan hispaniya, musulmi, da mata da mutane wadanda suke da larura iri daban daban."