Da yake ziyara a kasar Habasha, Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry, ya bayyana irin goyon bayan da Amurka zata bayar wajen gani an ceto daliban mata daga arewa maso gabashin Najeriya.
“Satar daruruwan dalibai da ‘yan bindiga sukayi laifi ne babba, kuma zamu yi duk abunda zamu iya domin taimakawa gwamnatin Najeriya, a mayarda wadannan yara zuwa wajen iyalansu, sannan a gurfanar da wadanda suka yi wannan laifi a gaban shari’a,” Sakatare Kerry yace a babban birnin Addis Ababa deke Habasha Asabar dinnan.
Biyo bayan sace daliban, hukumomin Najeriya, musamman ma Ma’aikatar Tsaron Najeriya ta fitar da sanarwa ta bakin kakakinta Chris Olukolade na cewa ta kubutar da kusan duka daliban, kalamun da iyaye da jami’an makaranta suka karyata, sannan daga baya hukumar ta janye kalamunta.
Mata a sassa daban-daban na Najeriya da ketare sun gudanar da zanga-zangar lumana domin kira ga gwamanti akan ta dauki matakin nemo wadannan dalibai, masu rubuta jarrabawar karshe a lokacin da aka sace su a manyan motoci a cikin dare.