Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga na Daura Aure da Daliban Cibok


Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace suna ganawa da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, a Chibok, jihar Borno, 22 Afrilu 2014.
Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace suna ganawa da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, a Chibok, jihar Borno, 22 Afrilu 2014.

Mutane da yawa sun shaida ana daurawa wasu daga cikin daliban Cibok aure da 'yan bindigan da suka sace su, a cewar wani dan majalisar Jihar Borno.

Dan majalisar wakilan tarayya dake wakiltar mazabar da ta hada da Monguna a Jihar Borno, Mohammed Tahir Monguno, yace rahotanni daga mazabarsa sun fada masa cewa an ga dalibai su sama da dari biyu da aka sace sama da makonni biyu kennan daga makarantar sakandare dake Cibok ana aurar dasu ga ‘yan bindigar da suka sato su, a gaban jama’a, har mutane da yawa suka shaida, kuma ya kara da cewa suma jami’an tsaro sun san da faruwar wannan lamari.

Dan majalisa Monguno ya kara da cewa daga inda aka sato daliban a Cibok, zuwa Shuwaram, tafiyar kusan kilomita 200 ne. Ya bayyana mamakinsa ga yadda aka yi tafiya mai wannan tsawo, ba tare da jami’an tsaro sun tsare su ba, a cikin jihar dake da dokar-ta-baci.

Daliban mata su 234, ‘yan ajin karshe ne dake rubuta Jarrabawar Fita daga Sakandare a Yammacin Afirka, ko WAEC a takaice a lokacin da ‘yan bindiga suka kaiwa makarantarsu farmaki cikin daren Litinin, sama da makonni biyu kennan, inda suka kona makarantar mallakar gwamnati baki dayanta, sannan suka kwashe daliban a cikin manyan motoci suka tafi dasu.

Hukumar tsaron Najeriya, ta bakin kakakinta Chris Olukolade ta fitar da sanarwar ceto kusan duka daliban, kalamun da iyaye da hukumomin makaranta suka musanta, kuma daga baya hukumar tsaron ta janye kalamunta. Ya zuwa yanzu dai bata sake bayanna wani mataki ko daya ba, akan irin aikin da takeyi na gani ta ceto daliban.

Shugaba Jonathan ya gudanar da taro Alhamis dinnan da duka gwamnoni, da shuwagabannin al-umma, da hukumomin tsaro game da batun tsaro, inda taron ya kayyade da bayanna matakai da za'a dauka domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Iyaye da ‘yan uwan daliban sun yi kokari da kansu su ceto matan, ta hawa babura sama da 150 domin bin sawun ‘ya’yansu, amma an gargade su akan cewa mutanen da suka sace daliban na dauke da makamai. A farkon makonnan ne kungiyoyin mata da iyayen sun yi taro suna kira a sako daliban. Wasu iyayen ma sun kuduri aniyar suyi zanga-zanga a Cibok domin nuna bacin ransu akan abunda suka kira rashin kulawa da lamarinsu daga hukumomi da jami'ai.

Gwamnatin Jihar Borno tayi alkawarin bada tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya bada wani bayani da zai kai ga ceto yaran mata.

A baya-bayannan ma, Gwamnan daya daga cikin jihohin dake da dokar-ta-baci, wato Jihar Adamawa, Murtala Nyako ya zargi da hannun gwamnati a rincabewar lamuran tsaro a arewarin Najeriya, zargin da gwamnati ta musanta, kuma wasu shuwagabanni a Najeriya da dama suka yi ta sukan gwamna Nyakon. Har yanzu tsohon hafsin rundunar sojin ruwa bai janye kalamunsa ba, wanda a ciki harda tattara shaidu na kaiwa kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa a birnin Hague, domin tuhumar Shugaba Jonathan da kisan kare dangi.

Jihar Borno dai na daya daga cikin jihohin dake fama da tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, inda ‘yan bindigar nan da aka fi sani da Boko Haram suke da karfi, wadanda suka fara tayar da kayar baya tun shekara ta 2009. Ya zuwa yanzu gwamnatin Najeriya tace zata shawo kan matsalar, amma kashe-kashen mutane da kone-kone bai tsaya ba.

A kwanakin baya, 'yan siyasa sun bayanna cewa Shugaba Jonathan na so ya sabonta dokar-ta-baci, amma 'yan majalisar na daura dammarar adawa da hakan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:37 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG