WASHINGTON, DC —
“Ina matukar damuwa da sace dalibai sama da 200 da ya faru a watan da ya wuce, a lokacin da suke cikin dakunansu na kwana a Cibok dake Jihar Borno a Najeriya. Zuciyata na tare da iyalen wadannan yara, kuma ina addu’a wadannan yara zasu koma wajen iyalensu,” inji Mr. Bass.
“’Yancin yara shime ‘yancin bil adama ne, kuma ire-iren wadannan hare-hare, musamman akan makarantu ya saba dokokin kasa da kasa, kuma baza a amince da shi ba a kowani irin yanayi. Makarantu wajen hutu ne da tsaro, inda yara zasu samu ilimi sannan su girma ba tare da fargabar wani ya cutar dasu ba. Yara mata da matasa a duk fadin duniya, dole sai an barsu sunyi karatu cikin kwanciyar hankali, ba tare da an razana su ba, da kuma kowace irin tsangwama.”
“Ina kira ga duk wanda yake da alhakin sace wadannan yara ya sake su nan take, ba tare da cutar dasu ba. Dole ne wadanda suka dauki yarannan su tabbatar daliban sun koma wajen iyalensu lafiya, inda ya kamata a ce suke.”
Har ya zuwa yanzu, babu tabbacin inda wadannan dalibai suke, hakan ya saka jama’a da dama a duk fadin Najeriya suka far zanga-zangar lumana domin kira ga hukumomi su dauki matakan neman daliban.
A bayannan kakakin ma’aikatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Chris Olukolade ya bada sanarwar ceto kusan duk daliban, kalaman da ya janye daga baya.
Iyayen wadannan daliban na cigaba da korafin cewa babu wani jami’in gwamnati ko hukuma da yace musu komai game neman yaransu, banda gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima wanda ya kai ziyara makarantar bayan faruwar lamarin.