WASHINGTON, DC —
Dattawan Borno sun ce kwato daliban da aka sace a garin Chibok kimanin makonni uku da suka gabata ba batun kawamiti ba ne kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi.
Sace daliban ya jawo hankulan kungiyoyi na cikin gida da na waje da ma gwamnatocin kasashen duniya da dama. Mutane na cigaba da tofa ayar tambaya akan makomar daliban wadanda har yanzu babu wanda ya san inda suke. Dalili ke nan da shugaban Najeriya ya kafa wani kwamiti domin ya binciki aukuwar lamarin. 'Yan kwamitin zasu ziyarci jihar ta Borno da garin Chibok domin jin yadda abun ya wakana.
Amma kungiyar dattawan jihar Borno tace lamarin ba batun kwamiti ba ne domin babu abun da kwamitin zai tsinanta masu. Abun da ya dace shi ne gwamnati ta cigaba da kara kaimi wurin gano inda aka shiga da daliban. Idan ba haka ba basu ga abun da kwamitin zai iya tabuka akan lamarin ba.
Dr Bulama Malugu Byo mai magana da yawun kungiyar dattawan yace abun ba na kwamiti ba ne. Yace ana neman 'yan mata kusan dari uku menene kwamitin zai iya yi. Shin wai menene kwamitin zai yi. Shin wai lamarin bai faru ba ne. Shin wai ba'a tafi da daliban ba ne. Byo yace ai duk an fadi yadda abun ya faru. Kafa wani kwamiti bata lokaci ne. Ya kara da cewa yana ganin ana son a kawo siyasa ne cikin rayuwar mutanen Borno. Yace ana siyasa da dalibansu da rayuwarsu da ma zamantakewarsu. Wasu an kone masu gidaje da kasuwanni da gonakai. Wannan bai nuna akwai shugabanci nagari ba. Yanzu shekara biyar suna cikin wannan tashin tashinar.
Usman Mustapha shugaban kungiyar dake neman kawo sauyi a arewacin kasar na jihohi 19 har da birnin Abuja yace sace daliban sakaci ne daga wurin jami'an tsaro. Mutanen garin sun shaida masu cewa lokacin da 'yan Boko Haram suka shiga garin jami'an tsaro gudu suka yi. Ban da haka 'yan Boko Haram sun kashi sa'o'i hudu suna kwashe yaran babu abun da jami'an tsaron suka yi.Yakamata a tambaya shin ina jami'an tsaron suka shiga. Kamata yayi shugaban kasa ya fito ya nemi gafara daga al'ummar kasar Najeriya cewa jami'an tsaro sun kasa.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.