Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Shettima ya Gana da Iyayen Cibok


Gwamna jihar Borno Kashim Shettima, a tsakiya lokaci da ya kai ziyara makarantar sakandare na Chibok. An dauki hoton nan 21 ga Afrilu 2014.
Gwamna jihar Borno Kashim Shettima, a tsakiya lokaci da ya kai ziyara makarantar sakandare na Chibok. An dauki hoton nan 21 ga Afrilu 2014.

A wani lamari mai ban tausayi, iyayen dalibannan mata da aka sace a garin Cibok a makon jiya, sun shaida wa gwamnan jihar Borno, Honourable Kashim Shettima cewa adadin ‘ya’yan nasu da aka sace 234 ne, kuma 34 ne suka kubuta, sabanin rahotannin dake fitowa daga hukumomin makarantar na cewa adadin daliban 129 ne.

Wadannan iyayen sun shaida wa gwamnan wannan batun ne a lokacin da ya kai ziyara garin na Cibok domin ganewa idanunsa irin barnar da aka yi a makarantar, da kuma jajantawa iyayen wadannan daliban.

Mr. Shettima ya soma ne da nuna juyayinsa ga iyayen wadannan yara, da kuma yi musu alkawarin cigaba da neman inda wadannan yara suke.

A lokacin da yake wa iyayen yaran jawabi, yana share hawaye daga idanunsa, yace “abunda ya same mu dinnan, ya shafi duk mutumin kasarnan. Ya shafi duk mutumin duniya. Yara ne basu san hawa ba, basu san sauka ba, sunzo neman ilimi, tsirarun yara suzo su debe su. Jami’an tsaro suna gwargwadon karfinsu, a yanzu haka ma suna gwagwarmayar kwato ‘ya’yanmu. Amma bai can-canta in bada bayani fiye da haka ba. InshaAllah, inshaAllah, inshaAllah za’a samu yarannan a cikin koshin lafiya. Dole mu baku hakuri, wannan masifa ce ta fado a kanmu, kuma in Allah Ya yarda, Allah Zai ceto mu.”

Shima dan majalisa mai wakiltar mazabar kudancin Borno Senata Muhammad Ali Ndume yayi wa iyayen jawabi cikin jimami da tausayawa kamar haka.

Senata Nduma yace “dalilin da muka zo nan, shine don ku sani, muna tare da ku, abunda ya same ku, ya same mu. Meye shugaba idan jama’arsa suna cikin kunci? Babu amfani! Mene ne shugaba idan kai kana da lafiya, wadanda kake shugabanci basu da zaman lafiya? Allah Ya jarrabce mu da wannan shugabanci a lokacin da mu dinma, babu abunda zamu iya yi, sai dai muyi jagora mu koma ga Allah mu roki Allah Ya kawo mana saukin wannan abun.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG