WASHINGTON, DC —
A ganawar da tayi da wasu matan Gwamnonin Najeriya a karshen makonnan, da kuma wasu mata daga garin Cibok, inda aka kwashe dalibai mata wadanda ke rubuta jarrabawar karshe, Mrs. Patience Jonathan ta zargi da hannun gwamnan Jihar Borno, Hon. Kashim Shettima a satar yaran.
Asabar dinnan ne Mrs. Jonathan ta gudanar da taron a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, inda tace laifin Kashim Shettima ne har ya kaiga sace yaran, kuma tace lallai shine ya kamata ya ceto daliban.
Kalamunta basu ban mamaki sune suka kunshi dorawa Gwamnan alhakin tsaron Jihar, a halin da ake ciki kuma, Bornon na karkashin dokar-ta-baci wanda ya mayar da hurumin tsaron Jihar hannun shugabancin kasa.
Manazarta kundun tsarin mulki na shakkar ko akwai tanadin daya bata ikon gudanar da taro irin wanda tayi Asabar dinnan.
Daga gefe kuma, majalisar dokokin Jihar Borno ta dorawa mijin Patience, wato Shugaba Jonathan alhakin satar daliban mata, inda ma ta bakin shugaban kwamitin yada labaranta Honorable Muhammad Sale Banga aka ji kalamai masu kaushi.
“Mu a Jihar Borno, da kuma Yobe, bazan tsaya a Borno kadai ba, ka ga wannan abu ya faru a FGC Buni Yadi a Jihar Yobe, sannan kuma aka debe wadannan daliban sama da dari biyu, to ana kan wannan ce-ce ku-ce, sai ga magana daga fadar shugaban kasa, tunda matar shugaban kasa ce, take cewa a gayawa Gwamnan Borno, Ya fito da wadannan ‘yan matan. To idan ba’a manta ba, akwai lokacin da gwamnan Bornon ya fito yake cewa mutanennan, wadannan ‘yan kungiyar suna da makamai fiye da jami’an tsaron kasa. Aka yi masa ca, a wannan lokacin,” a cewar Hon. Banga. “Hatta shi shugaban kasa, abunda ya furta yace da zai janye sojojinsa, gwamnan Borno bai isa ya shiga ofishinsa ba, bai isa ya shiga gidan gwamnati ba.”
Hon. Muhammad Sale Banga ya cigaba da cewa “yau bamu sani ba, janye sojojinnan yayi ne, sannan aka zo aka kwashe ‘yan matannan a makarantarnnan na Cibok? ko kuma a’a akwai jami’an tsaron da shugaban kasa ya baiwa Gwamnan na Borno, sannan shi kuma ya basu umarnin kwashe wadannan dalibai, sannan har tace shi Gwamnan Bornon ya dawo da daliban?”.
“Ai wannan magana, ana cewa idan mai magana wawa ne, maji magana ba wawa bane,” a cewar Hon. Banga. “Gaskiyar magana, ta (Matar shugaban kasa) tambayi fadar shugaban kasa, ta tambayi mijinta sannan ya saka jami’an tsaro, a matsayinsa na shine shugaban jami’an tsaron Najeriya baki daya, wato nan da ‘yan kwanaki kadan, ba tare da bata lokaci ba da gaggawa, yadda asiri yake tonuwa, asiri ya tonu, su fito da wadannan ‘yan matan.”
Yanzu dai misalin makonni uku kennan da sace daliban su sama da 200 a makarantarsu ta Sakandare a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe.
Shugaba Jonathan lahadinnan yayi alkwarin ceto daliban a ganawar da yayi manema labarai.
A halin yanzu dai jama’a sun share kwanaki 6 suna gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Abuja domin kira ga hukumomi su mayar da hankali wajen ceto wadannan yara.
Yanzu dai an tsare shugabar matan Cibok dake wannan zanga-zanga bayan ganawa da tayi da matar shugaban kasa a birnin na Abuja.