Yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare da ya yi sanadiyar karuwar asarar rayukan fararen hula, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a yi amfani da wani karfin ikon da ba kasafai ake amfani da shi ba a wannan makon.
Kungiyar vehicle for change na aiki da motocin da aka bayar gudummuwa, su gyara su, sannan da hadin gwuwar hukumomi daban-dabam a daukacin yankin da su ke, sai su gano iyalan da ke bukatar mota domin zuwa wurin aiki ko yin wasu al'amura na rayuwa a basu.
Sabuwar jakadiyar Amurka ta gabatar wa hukumomin rikon kwaryar Nijar takardun kama aiki, kwana daya bayan haka Rasha ta tura karamin ministanta na tsaro zuwa birnin Yamai, ziyarar da masana suka fassara a matsayin wani yunkuri na Rasha na samun matsuguni a Yankin Sahel.
Sandra Day O'Connor, wacce ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko mai shari'a a Kotun Koli, ta mutu da safiyar Juma'a ta na da shekaru 93.
Henry Kissinger, wanda ya rasu ranar Laraba yana da shekaru 100, ya bayyana manufofin harkokin wajen Amurka a zamanin gwamnatin Nixon da Ford, inda ya zama sakataren harkokin wajen kasashen waje a karkashin shugabannin biyu.
Ana sa ran sabuwar yarjejeniyar za ta kubutar da karin wasu mutane da aka yi garkuwa da su daga Gaza, yayin da Isra’ila za ta saki karin wasu Falasdinawa.
A yau Alhamis, Qatar ta sanar cewa dakatar da fada tsakanin Isra'ila da Hamas da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su da fursunoni na iya zuwa nan gaba kadan, bayan jinkirin aiwatar da yarjejeniya tsakaninsu wanda kuma hakan zai taimakawa agajin jin kai zuwa zirin Gaza.
Kungiyar jaruman fina-finan Hollywood ta cimma matsaya da kamfanonin hada fina-finai a ranar Laraba don kawo karshen yajin aikin da ta yi, wanda ya kawo kusan watanni na rikicin ma’aikata ya kuma kawo cikas ga masana’antar nishadi a tarihi.
Daruruwan dubban Falasdinawa ne suka rasa gidajensu sanadiyyar hare-haren saman da Isra’ila take kai wa kan Hamas a matsayin martanin harin da ta kai wa Isra’ilan.
Magajin garin Newark, New Jersey a Amurka, Ras J. Baraka, ya karrama Kanyeyachukwu Tagbo Okekene a ranar Lahadi da lambar yabo, a yayin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin Najeriya karo na 8 a jihar.
“Alamu sun nuna karara cewa yanzu ba lokacina ba ne.” In ji tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.