Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wata Kungiya Ke Sauya Rayukan Tsoffin Masu Laifi A Amurka


Alexis Austin
Alexis Austin

Kungiyar vehicle for change na aiki da motocin da aka bayar gudummuwa, su gyara su, sannan da hadin gwuwar hukumomi daban-dabam a daukacin yankin da su ke, sai su  gano iyalan da ke bukatar mota domin zuwa wurin aiki ko yin wasu al'amura na rayuwa a basu.

Vehicle for change wata kungiya ce da ta shafe shekaru 24 tana gudanar da ayyuka ba don neman riba ba dake taimakawa daurarru da mutanen da suka kammala zaman gidan kaso. Babban abin da suke yi shine tunkarar manyan al’amurra biyu da suka shafi tsarin shari’a da banbancin launin fata da ake nunawa a zaman sarka.

Sun tsara shirin da kungiyar ke gudanarwa ne shekaru 24 da suka wuce, inda suke samar da motocin hawa ga iyalai da ke rayuwa cikin talauci, da ke bukatar samun hanyar aikin yi.

Su kan samu motocin da aka bayar gudummuwa, su gyara su, sannan da hadin gwuwar hukumomi dabam dabam a daukacin yankin da suke sai su gano iyalan da ke bukatar mota domin zuwa wurin aiki.

Ana nan ana nan, suna ci gaba da haka, sai kungiyar ta gano cewa, a tsarin gidan kurkuku na jihar Maryland dake Amurka suna da wani, tsarin bayar da horo. Sai kungiyar ta Vehicle for change, ta ga lallai wannan kyakkyawan tsari ne da za su iya amfani da shi, su kuma yi aiki tare da jihar ta Maryland, domin su kawo irin wadannan mutanen su samu karin horo na watanni hudu. Saboda haka suna nan a yanzu suna samu horo da kayayyakin kungiyar.

Daga nan idan daurarrun suka kammala samun horon, sai kungiyar ta samar masu aikin yi daga abokan huldar su dake ko’ina a yankin.

Daya daga cikin irin wadannan tsoffin daurarrun ita ce mai suna Alexis Austin, wadda ta ce, ta hadu da kungiyar Vehicles for change ne kimanin shekaru 7 da suka wuce. Ta ce su 6 aka ya ye, kuma ko wannen su ya yi nasara. Ta bayyana cewa, ita makanikiyar gyranan motoci a inda take.

Idan ta gaya ma mutane cewa ita makanikiya ce, sai hakan ya rika burge su. Kamar basu taba ganin mace na gyaran mota ba kamar yadda ta ke yi. Ta dawowa gida ne bayan shafe shekaru 5 a gidan kaso.

Ta samu labarin kungiyar Vehicle for change ne tun tana daure, kuma a dai dai lokacin da ta cikin wani yanayi na tunanin abinda za ta yi da rayuwar ta.

Alexis ta ce, a matsayin wurin na koyon ayyuka da bayar da horo, kuma mutum bai san komi ba game da gyaran motoci, za a koya maka komai tun daga fari, a fara da yadda ake canza taya, da batir, muhimman abubuwa dai haka. Sannan, kana saka kafa a wurin, zaka ga inda aka rubuta, SHIRIN BAYAR DA DAMA TA BIYU’ abin da ta ce, a gare ta, lallai wannan dama ce ta biyu.

A ranar da Alexis ta cika kwanaki hudu a wurin ne ta koyi yadda ake gane, abinda ake ce ma, ball joint, sannu a hankali ta cigaba da koyon abubuwa da dabam dabam, kamar koyon yadda ake gano indicator lights. Da dai sauran su.

Ta ce, ba wai kawai ta samu horo a aikin hannu ba ne, amma ta samu horo ne, kan yadda zata rike iyali, saboda abinda suka koya a karkashin shirin Vehicle for change, abu ne da zai canza rayuwa.

Ta kara da ce wa, mutanen dake fitowa daga sarka, su na zama ma’aikata na gari matuka. Su na kuma son yin aiki, da jin dadin damar da suka samu. Dama ce, mai ban sha’awa matuka na yin irin wannan aikin tare da wadannan mutanen. Wata kofa ce aka bude mana, da zamu bi ta zuwa ga samun cigaba.

A karshe Alexis ta kara da cewa, tana da gurin da sannu a hankali, itama ta bude nata garejin, wanda akasari zai kunshi mata makanikai zalla .Ta ce, hakika Vehicles for change, ya samar ma su da ilmin kanikanci daya ratsa ruhi ta, da ya zaburar da ita cikin al’ummar ta, ta zama mutuniyar kirki, mai kwarin guiwa, da karfafa tia a matsayin ta na mace.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG