Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Henry Kissinger, Tsohon Babban Jami'in Diflomasiyyar Amurka A Karkashin Nixon, Ya Mutu Yana Da Shekara 100


Henry Kissinger, Tsohon Babban Jami'in Diflomasiyyar Amurka A Karkashin Nixon
Henry Kissinger, Tsohon Babban Jami'in Diflomasiyyar Amurka A Karkashin Nixon

Henry Kissinger, wanda ya rasu ranar Laraba yana da shekaru 100, ya bayyana manufofin harkokin wajen Amurka a zamanin gwamnatin Nixon da Ford, inda ya zama sakataren harkokin wajen kasashen waje a karkashin shugabannin biyu.

Ya kuma sha yabo na nasarorin diflomasiyya da kuma cece-kuce kan yadda ya tafiyar da siyasa a duniya.

Kamfanin sa ne ya sanar da rasuwarsa kuma ba a bayar da wani dalili ba.

Za a cigaba da alakanta tsohon sakataren harkokin wajen Amurka har abada da shugaba Richard M. Nixon, musamman ma ga kokarin da suka yi a fannoni uku: fitar da Amurka daga yakin Vietnam, bude huldar diflomasiyya da kasar China da kuma rage zaman dar-dar da Tarayyar Soviet.

Richard Nixon tare da Henry Kissinger.
Richard Nixon tare da Henry Kissinger.

An san shi a matsayin babban masani, wanda ya ci lambar yabon Nobel ta zaman lafiya kuma fitaccen ɗan gudun hijira a Amurka.

Mai tunanin ra'ayin mazan jiyan ya taimaka wajen samar da ɗimbin nasarorin diflomasiyya, gami da gyara dangantaka da China da kuma tsare Tarayyar Soviet.

An ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel tare da Le Duc Tho na Arewacin Vietnam saboda kokarin da suka yi na bada shawarwarin kawo karshen yakin Vietnam.
Kissinger kuma ya sami nasarori da yawa a Gabas ta Tsakiya, gami da bada shawarwari kan yarjejeniyar Sinai ta 1975 tsakanin Masar da Isra'ila, da kuma aikin da ya yi wajen samun cigaba ga tsarin zaman lafiya tsakakin Larabawa da Isra'ila.

Sakatare Janar na Tarayyar Soviet da Henry Kissinger a Moscow
Sakatare Janar na Tarayyar Soviet da Henry Kissinger a Moscow

Duk da nasarorin da ya samu a fadin duniya, Kissinger ya kasance mutum mai cike da cece-kuce, inda masu sukar suka yi zargin cewa ya rufe ido yayin ruwan bama bamai da aka kai kan wani bangaren Cambodia, ya kuma goyi bayan Pakistan ta murkushe Bangladesh, kuma bai yi wani yunkurin hana Argentina yakin da ta yi da ‘yan adawa ba.

An kuma soki Kissinger saboda rawar da ya taka a tashe-tashen hankula a duniya, ciki har da yakin basasar Angola, wanda ya zama fagen yakin cacar baki, da kuma tsoma bakin Amurka a Chile, wanda ya kai ga juyin mulki a 1973.

An haifi Kissinger Heinz Kissinger ne a Furth, Jamus, ranar 27 ga watan Mayun 1923, cikin wani iyali na matsakaita waɗanda suka kasance Yahudawa a jihar Bavaria.

Daga baya iyalan suka tserewa gallazawar ƴan Nazi, sai dai sun shiga cikin iyalan Jamus Yahudawa a birnin New York a 1938.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG